Bidiyon faston Najeriya yana tada matacce ya janyo cece-kuce

Bidiyon faston Najeriya yana tada matacce ya janyo cece-kuce

- Wani bidiyon faston Najeriya mai cike da abun mamaki da al'ajabi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon, an ga faston yana addu'a a kan wata mata da ta mutu har aka saka ta a akwatin gawa

- Bayan wani lokacin da ya shafe yana addu'a, an ga matacciyar matar ta tashi tsaye tare da fitowa daga akwatin gawar

Wani faston Najeriya ya janyo cece-kuce bayan wani bidiyonsa ya watsu a kafafen sada zumuntar zamani, shafin linda Ikeji ya wallafa.

A bidiyon mai cike da al'ajabi da abun mamaki, an ga faston yana tada wata mata da ta mutu a cikin cocinsa, inda ta mike garas bayan mutuwarta.

An ga matar da farko a cikin akwatin gawa, inda aka rufe fuskarta da wani farin abu yayin da faston ke mata addu'a.

An hango wasu daga cikin mambobin cocin suna rera wakoki daga bayan faston kafin daga bisani matar ta tashi daga cikin akwatin gawar.

Hakan kuwa ya janyo cece-kuce mai tarin yawa a kafafen sada zumuntar zamani inda wasu ke kallon hakan a matsayin mu'ujizar bogi.

Bidiyon faston Najeriya yana tada matacce ya janyo cece-kuce
Bidiyon faston Najeriya yana tada matacce ya janyo cece-kuce. Hoto daga shafin Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda jirginmu ya kusa ragargajewa a sararin samaniya - Aisha Buhari

A wani labari na daban, wani babban fasto mai shekaru 57, mai suna Ebenezer Ogunmefun, ya shiga hannun 'yan sanda kuma an gurfanar da shi a gaban wata kotun majistare da ke zama a Abeokuta.

Ana zargin babban faston da yi wa yarinya mai shekaru 15 fyade, wacce mahaifiyarta ta kai ta cocin don tsarkakewa.

A yayin da aka gurfanar da faston a kan zargin cin zarafi, dan sanda mai gabatar da kara, sifeta Moshood Hammed, ya sanar da kotun cewa faston yana zama ne garin Abeokuta.

Faston na zama a gida mai lamba daya, titin Farfesa Ajibo Toluca a yankin Olomore da ke Abeokuta a jihar.

Ya sanar da cewa mahaifiyar yarinyar da kanta ta mika ta ga faston domin 'tsarkakewa' daga miyagun aljanu.

Faston ya sa yarinyar ta yi rantsuwa da bibul cewa ba zata sanar da kowa cewa ya yi mata fyade ba yayin da yake raba ta da miyagun aljannun.

Dan sanda mai gabatar da kara, ya ce laifin ya ci karo da sashi na 33 na dokokin hakkin kananan yara na jihar Ogun na 2006.

Duk da faston ya musanta aikata laifin, alkalin ya bada belinsa daga bisani, tare da dage sauraron shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Satumban 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel