Imam Mahmoud Dicko: Ɗan siyasar da ya janyo juyin mulki a kasar Mali

Imam Mahmoud Dicko: Ɗan siyasar da ya janyo juyin mulki a kasar Mali

An ruwaito cewa idan har shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasahen Afirka ta Yamma, ECOWAS, suna son samar da zaman lafiya a Mali da aka yi juyin mulki a kwanan nan, ya zama dole su yi sulhu da wani mutum mai suna Imam Mahmoud Dicko.

Legit.ng ta ruwaito cewa an ce Dicko ne ke jagorancin boren da aka kwashe watanni biyu ana yi don nuna rashin amince da Shugaba Boubacar Keita.

Har wa yau, daga bisani ya nuna goyon bayansa ga masu juyin mulkin bayan sun hambarar da Keita a ranar Talata 18 ga watan Agusta.

Imam Mahmoud Dicko: Dan siyasar da ya janyo juyin mulki a kasar Mali
Imam Mahmoud Dicko: Dan siyasar da ya janyo juyin mulki a kasar Mali
Asali: UGC

Hujja da za a iya kafa wa game da wannan ikirarin shine yadda shugabannin masu adawa da gwamnatin, M5-RFP, suka dauki babban malamin addinin musuluncin a matsayin jagoransu a addinance kamar yadda PM News ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Kazalika, Dicko, a ranar Jumaa 21 ga watan Agusta ya jagoranci jiga jigan M5-RFP, a wata taro da suka yi a Bamako na nuna goyon baya ga sojojin kasar da suka yi juyin mulki, abinda masu adawa da Keita ke yi wa kallon nasara ce gare su.

Sai dai, babban malamin na addinin musulunci mai fada a ji, ya yi kira ga mutane su zauna lafiya a jawabinsa a wurin taron kuma ya bukaci ya yafe wa Keita.

Ya nuna rashin jin dadinsa game da barna da asarar dukiyoyi da aka yi a kasar ta Mali inda ya shawarci alumma su zauna lafiya.

Ya ce, "Mali ba kasar ramuwar gayya bace. Kasa ce na fahimtar juna. Ya zama dole mu hada kai wuri guda domin fatattakar shedannin da ke raba kanmu da saka mana kiyayya. Lokaci ya yi."

A wani rahoton, Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'a ta ce ta samu ganin hambararren Shugaban Mali a yayin da masu tayar da kayan bayan suka ce sun sako mutum biyu cikin wadanda suka tsare bayan kasashen duniya sun matsa musu lamba.

"A daren jiya, wata tawaga daga MINUSMA, kungiyar kare hakkin bil adama ta tafi Kati a yunkurin aikinta na kare hakokin yan adam kuma ta samu ganin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da wasu da aka tsare," a cewar tawagar samar da zaman lafiya ta UN.

Kati sansanin sojoji ne da ke kusa da babban birnin kasar, Bamako inda ake tsare da wadanda aka kama yayin juyin mulkin da aka yi a ranar Talata a kasar ta Mali da aka dade ana rikici.

Kazalika, wani majiya da ya nemi a boye sunansa ta ce ta bawa "tawagar UN" izinin zuwa su gana da dukkan fursunonin 19 da ke tsare a Kati ciki har da Keita da Farai minista, Boubou Cisse.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel