Matar da ta haihu kuma ta jefa jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna)

Matar da ta haihu kuma ta jefa jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna)

An kama wata mata mai shekaru 30, Franca Udokwu saboda ta jefa jinjirin da ta haifa a cikin masai a garin Obuba Obofia Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta arewacin jihar Anambra.

An ce wacce ake zargin ta jefa jinjirin cikin masai ne a dakin ta bayan ta haihu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa yan sanda sun gano jinjirin bayan an sanar da su amma ko da suka isa asibiti da ke kusa da gidan matar jinjirin ya mutu.

Matar da ta jefe jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna)
Matar da ta jefe jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna). Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, mai magana da yawun yan sandan jihar Anambra, Haruna Mohammed ya ce an kama wacce ake zargin kuma za a gurfanar da ita a kotu idan an kammala bincike.

Matar da ta jefe jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna)
Matar da ta jefe jinjirin ta cikin masai ta shiga hannu (Hotuna). Hoto daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Ya ce, "a ranar 22/8/2020 misalin karfe 8:30 na safe bayan an kai musu rahoto jamian yan sanda da ke ofishin Ogidi sun kama wata Franca Udokwu mai shekaru 30 yar garin Obuba Obofia Nkpor da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

"Wacce ake zargin ta haifi da na miji sannan ta jefa shi cikin masai a gidanta.

"Bayan an mata tambayoyi, wacce ake zargin da nuna wa yan sanda inda ta jefa jinjirin kuma aka ciro shi aka mai shi asibitin Iya enu don bashi kulawa amma da suka isa likita ya tabbatar ya mutu.

"A halin yanzu an aki gawar jinjirin dakin ajiye gawarwakin don yin gwajin tabbatar da sanadin mutuwarsa yayin da za a cigaba da bincike daga bisani kuma a gurfanar da wacce ake zargin a kotu."

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Yan sanda a jihar Borno sun ceto wani yaro mai shekaru 13 da mahaifinsa da matansa biyu suka rika cin zarafinsa na tsawon lokaci.

Mai aikin jin kai, Junaid Jibril Maiva wanda ya wallafa labarin a dandalin sada zumunta ya ce mahifin Aminu ya rabu da mahifiyarsa amma shi yaron ya cigaba da zama tare da mahaifin.

Mahaifin da matansa ba su bashi abinci da sauran kulawa kuma balantana muhallai mai kyau inda wani daki kusa da kwata ya ke kwana.

Bayan samun bayannan sirri, yan sanda sun dira gidan mahaifin a Baga road a Maiduguri babban birnin jihar Borno suka ceto shi.

Mahaifinsa da matansa a halin yanzu suna hannun yan sanda.

Ga wani sashi cikin abinda Junaidu ya wallafa a Facebook.

"Abin bakin ciki ne yadda wasu iyaye ke kin kulawa da yaran da suka haifa. An dena kula da wani yaro mai shekaru 13 saboda kawai mahaifinsa ya saki mahaifiyarsa.

"An tilasta masa kwana a baranda kusa da kwata babu abinci ko tufafi balantana gidan sauro domin kare kansa daga zazzabin cizon sauro."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel