Bidiyo da hotunan yaron da mahaifinsa da matansa suka rika azabtar da shi a Borno

Bidiyo da hotunan yaron da mahaifinsa da matansa suka rika azabtar da shi a Borno

Yan sanda a jihar Borno sun ceto wani yaro mai shekaru 13 da mahaifinsa da matansa biyu suka rika cin zarafinsa na tsawon lokaci.

Mai aikin jin kai, Junaid Jibril Maiva wanda ya wallafa labarin a dandalin sada zumunta ya ce mahifin Aminu ya rabu da mahifiyarsa amma shi yaron ya cigaba da zama tare da mahaifin.

Mahaifin da matansa ba su bashi abinci da sauran kulawa kuma balantana muhallai mai kyau inda wani daki kusa da kwata ya ke kwana.

Bayan samun bayannan sirri, yan sanda sun dira gidan mahaifin a Baga road a Maiduguri babban birnin jihar Borno suka ceto shi.

DUBA WANNAN: Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Mahaifinsa da matansa a halin yanzu suna hannun yan sanda.

Ga wani sashi cikin abinda Junaidu ya wallafa a Facebook.

"Abin bakin ciki ne yadda wasu iyaye ke kin kulawa da yaran da suka haifa. An dena kula da wani yaro mai shekaru 13 saboda kawai mahaifinsa ya saki mahaifiyarsa.

"An tilasta masa kwana a baranda kusa da kwata babu abinci ko tufafi balantana gidan sauro domin kare kansa daga zazzabin cizon sauro."

Mahaifin yaron, Mallam Murtala dan asalin karamar hukumar Mobbar da ke zaune a Baga road, Maiduguri ya bayyana cewa shi da matansa suna bawa yaron abinci sau daya a kullum.

Yayin binciken da hukumar kiyayye hakkin bil adama karkashin jagorancin Barr Jummai Mshelia suka yi an gano cewa matar mahaifin Aminu su kan doke shi ba tare da wani kwakwaran dalili ba.

Anyi mamakin ganin yadda Aminu ke cin abinci cikin gaggawa wadda alama ce da ke nuna ya dade bai samu abinci ba kawai domin mahaifiyarsa ba ta gidan.

Bayan an kammala rubuce rubuce, za a garzaya da Amunu asibiti domin likita ya duba shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel