Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

Hotuna: Jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas

- Wani hadarin jirgi mara muni ya faru a filin tashin jirage na Murtala Mohammed da ke Legas

- Lamarin ya faru ne bayan wani karamin jirgi ya yi karo da wani katanga mallakar Bristow Helicopters

- Jirgin ya yi karo da katangar ne sakamkon birkinsa ya ki yin aiki

Wani jirgin sama mallakar King Air Jet, ya yi hatsari a katangar filin tashin jirage na Legas a ranar Juma'a 21 ga watan Agusta bayan birkinsa ya lalace.

Mobil Oil Nigeria-Wings ne ke da jirgin kirar King Air 200 mai lamba 5N-HIS.

Wani shaidan ganin ido ya ce;

"Hatsarin ya afku ne misalin ƙarfe 10 na safe a titin jirgin sama kusa da filin ajiye jirgi masu saukar ungulu ta Bristow. Birkin jirgin ya dena aiki hakan yasa jirgin ya yi karo da bangon wurin ajiye jirgi mai saukan ungulu," in ji shaidan ganin idon.

Hukumar binciken hatsari (AIB) ta ce an fara gudanar da bincike domin gano abinda ya yi sanadin afkuwar hatsarin.

Ga wasu hotunan hatsarin jirgin a kasa;

Hotunan jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas
Hotunan jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji

Hotunan jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas
Hotunan jirgin saman da ya yi karo da katanga a Legas. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

A wani rahoton da Legit.ng Hausa ta wallafa, kun ji a ranar Juma’a, 24 ga watan Yulin 2020, filayen tashi da saukar jiragen sama 14 gwamnatin tarayya ta amince da su koma aiki.

Sannan a ranar 8 ga watan Yulin 2020 ne gwamnatin tarayyar ta bude filayen sauka da tashin jiragen sama na Legas da Abuja.

Har ila yau a ranar 11 ga watan Yuli aka bude filayen jiragen sama hudu da suka hada da na Fatakwal da ke jihar Ribas, filin sauka da tashin jiragen sama na mallam Aminu Kano, Maiduguri da kuma Owerri.

Kungiya daga hukuma kula da kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu, sun dudduba filayen sauka da tashin jiragen saman kafin budesu.

Daya daga cikin abubuwan da suka duba kafin amincewa da bude filayen sauka da tashin jiragen saman shine tabbatar da dokokin dakile yaduwar muguwar annobar korona tare da tabbatar da tsafta.

Darakta Janar na NCCA, Kyaftin Musa Nuhu ya ce akwai yuwuwar kungiyar NCAA din ta kwashe mako daya tana duba sauran filayen sauka da tashin jiragen saman kafin a budesu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel