Daga karshe, El-Rufa'i ya amince da bude Masallatan khamus-salawaati a Kaduna

Daga karshe, El-Rufa'i ya amince da bude Masallatan khamus-salawaati a Kaduna

Bayan watanni biyar, Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ya dage dokar hana Sallah a a Masallatan khamsu-salawati da zaman coci-coci a fadin jihar.

A takardar da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya rattafa hannu, ya ce an yanke dage dokar ne bisa shawarar kwamitin yaki da cutar Korona a jihar, Daily Trust ta samu rahoto.

Jawabin yace wajibi ne a rika bin dokokin da aka gindaya wanda ya hada da "sanya takkunkumin rufe fuska, baiwa juna tazara, tsafta, wanke hannu, nisanta taron jama'a masu yawa, cin abinci mai kara karfin garkuwa jiki, da zama a gida."

Gwamnatin ta yi gargadin cewa "wuraren ibadan da suka sabawa ka'idoji da sharrudan da aka kindaya na iya fuskantar sake rufewa domin kare rayukan jama'a."

Gwamnatin jihar ta sanya dokar kulle Masallatai da coci-coci a jihar Kaduna rranar 26 ga Maris 20220, doin takaita yaduwar cutar Korona.

Daga baya aka sassauta dokar inda aka amince Musulmai su halarci Sallar Juma'a kadai kuma Kirista su hallarci Coci ranar Lahadi kadai.

Daga karshe, El-Rufa'i ya amince da bude Masallatan khamus-salawaati a Kaduna
El-Rufa'i
Asali: Twitter

A bangare guda, Kungiyar Lauyoyin Najeriya, shiyar Jihar Jigawa, ta yi barazanar fasa halartar taron gangamin yanar gizon da uwar kungiyar ta shirya sakamakon janye gayyatar da ta yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Shugaban kungiyar NBA Dutse, Garba Abubakar, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Kungiyar ta bayyana cewa zarge-zargen da suke yiwa El-Rufa'i shirme ne kawai saboda ba'a bashi damar kare kansa ba kuma saboda haka, ba zata halarci taron da aaka shirya ba.

A jiya, Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.

NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa'i a cikin manyan baki da za su gabatar jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel