An damke yan kasar Nijar 3 masu safarar makamai a jihar Sokoto
Wasu yan kasar Nijar uku sun shiga hannu a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sakamakon safarar makami da fasa kwabri.
Jagoran yada labaran hukumar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan ranar Juma'a a hira da manema labarai.
Enenche ya ce mutanen uku mambobin wata kungiyar masu safara makamai ne a yankin
Ya bayyana cewa suna shigo da makamai Najeriya ta hanyar boyesu cikin motocinsu.
"Dakarun Operation SahelSanity da aka tura karamar hukumar Sabon Birni ranar 15 ga Augusta sun samu nasarar wargaza wani gungun masu safarar makamai da suka kware wajen kaiwa yan bindigan Arewa maso yammacin Najeriya makamai daga kasashen ketare."
"Dukkan mutane ukun yan kasar Nijar ne kuma an kamasu ne a Dantudu dake karamar hukumar Sabon Birni da bindigar AK-47 guda shida, carbin AK-47 hudu da harsasai 2,415 boye cikin motocinsu." Enenche ya laburta.
Kakakin hukumar tsaron ya kara da cewa matsalar rashin tsarona wasu sassan Najeriya na da sa hannun kasashen waje.
Enenche ya tuna cewa an damke wasu turawa biyu masu safarar makamai a jihar Nijar.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Muna bayan El-Rufa'i, ba zamu hakarci taronku ba - Kungiyar Lauyoyi NBA na Jigawa sun yi uwar kungiyar martani
Jihar Sokoto na fusktantar hare-haren yan bindiga kwanakin nan, na kusa shine wanda aka kai ranar 17 ga Agusta a karamar hukumar Sabon Birni.
Kwanaki hudu da suka gabata, an damke wasu masu fasa kwabrin makami - Alhaji Adamu Alhassan, Salisu Adamu da Abdullahi Sani.
Mutane ukun yan kasar Nijar ne.
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa makaman da suke dauke da shi wadanda aka nufi kai yan bindiga ne a karamar hukumar Isah a jihar Sokoto.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng