WAEC ta kama malaman da suka fitar da amsoshi da tambayoyin jarrabawar 2020
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare na Afirka Ta Yamma, WAEC, ta yi ikirarin cewa wasu daga cikin masu kula da jarrabawar ta ne suka fitar da tambayoyi da amsoshin jarrabawar kafin daliban su fara.
Shugaban ofishin hukumar WAEC na kasa, Patrik Areghan ne ya sanar da hakan a ranar Laraba kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Areghan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar sa ido da suka kai a wasu makarantu a unguwar Yaba da ke jihar Legas.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta
Ya tabbatar da cewa tuni an kama masu kula da jarrabawar da ke da hannu kuma ya gargadi dalibai su guji aikata duk wani abu mai alaka da magudin jarrabawa.
"Bai dace dalibai su bazama suna neman takardar jarrabawa ba da ake kira expo. Wannan abin kunya ne, Masu kula da jarrabawa suna karbar tamabayoyin jarrabawa daga WAEC suna zuwa wani wuri suna bude tambayoyin.
"Jiya mun kama wani a Nasarawa. Ba su san muna da tsarin yadda za mu bi mu gano su ba. A Bauchi ma mun kama guda daya. Daga nan muka gano shi. A Fatakwal ma wani dalibi da ya aikata hakan ya shiga hannu," in ji Areghan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng