Muna bayan El-Rufa'i, ba zamu halarci taronku ba - Kungiyar Lauyoyi NBA na Jigawa sun yi uwar kungiyar martani

Muna bayan El-Rufa'i, ba zamu halarci taronku ba - Kungiyar Lauyoyi NBA na Jigawa sun yi uwar kungiyar martani

Kungiyar Lauyoyin Najeriya, shiyar Jihar Jigawa, ta yi barazanar fasa halartar taron gangamin yanar gizon da uwar kungiyar ta shirya sakamakon janye gayyatar da ta yiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Shugaban kungiyar NBA Dutse, Garba Abubakar, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Kungiyar ta bayyana cewa zarge-zargen da suke yiwa El-Rufa'i shirme ne kawai saboda ba'a bashi damar kare kansa ba.

Yace: "Wani sashen kasar nan ba zasu raina mana hankali ba saboda dukkanmu muna da fahimtar doka."

"Saboda haka, muna kira ga shugaban kungiya na kasa, Paul Usor o (SAN) ya janye wannan shawara da gaggawa saboda idan ba haka ba, NBA Dutse ba zata halarci taron gangamin yanar gizon da ake shirin yi nan da kwanaki ba."

Muna bayan El-Rufa'i, ba zamu hakarci taronku ba - Kungiyar Lauyoyi NBA na Jigawa sun yi uwar kungiyar martani
Muna bayan El-Rufa'i, ba zamu hakarci taronku ba - Kungiyar Lauyoyi NBA na Jigawa sun yi uwar kungiyar martani
Asali: Twitter

KU KARANTA: Anambra: Chris Ngige da APC su na tare da Gwamna Obiano a kan dakatar da Sarkin Alor

A jiya, Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta janye gayyatar da ta yi wa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta bayan wasu daga cikin mambobin kungiyar sun nuna rashin amincewarsu.

NBA, wacce ta saka sunan El-Rufa'i a cikin manyan baki da za su gabatar jawabi a wurin taron, ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi masa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis.

"Shugabannin kungiyar NBA sun gana tare da yanke shawarar janye gayyatar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, zuwa wurin babban taronta na shekarar 2020 kuma za a sanar da gwamnan wannan shawara ta hannun kwamitin tsare-tsare," a cewar sanarwar.

Kimanin mutane 3,150 ne suka rattaba hannu a kan takardar nuna rashin amincewa da gayyatar El-Rufa'i zuwa wurin taron NBA wacce wani lauya, Usani Odum, ya rubuta domin yin korafi a kan gayyatar gwamnan.

A wata takarda daban da Farfesa Koyinsola Ajayi, shugaban kwamitin tsare-tsare na taron NBA, ya fitar a kan neman a janye gayyatar El-Rufa'i, ya bayyana cewa wasu lauyoyi sun bayyana cewa sam gwamnan ba zai yi magana a wurin taron ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel