COVID-19: Minista a Ireland ya yi murabus don ya hallarci taro

COVID-19: Minista a Ireland ya yi murabus don ya hallarci taro

Farai ministan Irelanda a ranar Juma'a ya karbi murabus din ministan noma, Dara Calleary bayan mutane sun nuna bacin ransu game da wani taro da ya hallarta inda ya saba dokokin kiyaye yaduwar korona.

Calleary ya nemi afuwa a ranar Alhamis saboda hallartar taron cin abincin da ya yi da kungiyar masu wasar golf na majalisar kasar ta shirya kwana daya bayan gwamnatin kasar ta tsaurara dokar hana yawo sakamakon yaduwar cutar.

Ireland na cikin kasashen da ke da dokoki masu tsauri a kan dakile korona inda mutane a makon nan muka rika sukar wasu dokokin gwamnatin na hana taron mutane fiye da shida ko da a cikin gida ne.

COVID-19: Minista a Ireland ya yi murabus don ya hallarci taro
COVID-19: Minista a Ireland ya yi murabus don ya hallarci taro. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

Mutane fiye da 80 ne suka hallarci taron ciki har da kwamishian kasuwanci Phil Hogan da wasu yan siyasa kwana daya bayan majalisar kasar ta sanar da tsaurara matakan dakile yaduwar cutar.

DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

Farai minista Micheál Martin cikin wata sanarwa ya ce kuskure ne hallartar taron da ya yi.

"Na karbi murabus din sa; Matakin da ya dauka shine ya fi dacewa da kasar a yanzu na yin murabus.

"Mutane da dama a kasar sun sadaukar da kansu sun jure wuya da kunci a bangaren kasuwancinsu da iyalansu domin biyayya da dokokin dakile yaduwar COVID 19.

"Bai dace a gudanar da taron yadda aka yi shi ba," a cewar Martin.

Bayan da Calleary ya wallafa sakon neman afuwa a Twitter, mutane fiye da 2,000 sun yi tsokaci a kan sakon cikin awa biyu, mafi yawancinsu na nuna bacin ransu kan cewa sun ki hallartar aure da jana'iza da sauran wasu tarurruka.

Jaridar Irish Times ta ruwaito cewa wani da ya nemi a sakayya sunansa da ke otel din da aka yi taron ya ce mahalarta taron ba su bayar da tazara ba, kuma sun gaisa da hannu kana ba su saka takunkumi ba.

An nada Calleary ministan noma ne a watan Yulin wannan shekarar bayan an kori magabacinsa saboda ya yi tukin mota cikin maye kimanin sati biyu bayan kafa gwamnatin Martin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel