Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji

Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji

Sabbin mahukunta a ƙasar Mali da suka naɗa kansu bayan yin juyin mulki a kasar suna tattauna yiwuwar mayar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da ake tsare da shi ƙasar Senegal, kamar yadda wata majiya daga sojin Mali ta fada wa Sputnik.

"Ana tattauna da kasar Senegal kan yiwuwar aike wa da shi (Keita) zuwa ƙasar ta Senegal," kamar yadda majiyar ya fadi a ranar Alhamis.

An fara juyin mulkin ne a ranar Talata a wani sansanin soji da ke Kati kusa da babban birnin kasar Mali wato Bamako.

Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji
Za a aiƙe da Boubacar Keita zuwa Senegal - Soji. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

Masu tayar da ƙayan baya a ƙasar sun tsare Firai minista Boubou Cisse da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin kasar.

Daga bisani Keita ya sanar da murabus dinsa tare da rushe majalisar ƙasar.

Shugabannin masu tayar da ƙayan bayan sun kafa kwamiti na ceto ƙasa a matsayin sabon gwamnati a kasar.

Kungiyar inganta tattalin arzikin kasashen Afirka, ECOWAS, a ranar Alhamis ta fara shirin aike wa da wata tawaga mai ƙarfi zuwa Mali a ranar Alhamis domin dawo da doka da oda.

ECOWAS na son a mayar da Keita matsayinsa na Shugaban ƙasar ta Mali kamar yadda Sputnik da NAN suka ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel