Dalilin da ya sa APC za ta samu nasara a zaben Ondo - Sanwo-Olu

Dalilin da ya sa APC za ta samu nasara a zaben Ondo - Sanwo-Olu

- Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da zai sa dan takararta, Gwamna Rotimi Akeredolu zai lashe zaben jihar Odo a ranar 10 ga watan Oktoba

- Jam'iyyar ta dora alhakin nasarar akan irin ayyukan da gwamna Akeredolu ya shimfida a sassan jihar, da suke bunkasa rayuwar jama'a

- Akwai dai manyan jam'iyyu guda 3 da suka fi daukar hankali a zaben, sune Mr Akeredolu daga APC, Eyitayo Jegede daga PDP da kuma Agboola Ajayi daga ZLP

Shugaban yakin zaben jam'iyyar APC a zaben jihar Ondo, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos, ya bayyana dalilin da zai sa APC za ta lashe zaben a ranar 10 ga watan Oktoba.

Mr Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Shugaban yakin zaben ya ce gwamnan jihar Ondo mai ci a yanzu, Rotimi Akeredolu, mai neman tazarce, ya yi kokari sosai da zai ba shi nasara mai yawa a zaben.

"Jam'iyyar ta dora alhakin nasarar akan irin ayyukan da gwamna Akeredolu ya shimfida a sassan jihar, da suke bunkasa rayuwar jama'a."

Mr Sanwo-Olu ya ce gwamnan mai ci a yanzu ya fitar da jihar Ondo daga mawuyacin hali zuwa tudun mun tsira, a yanzu jihar ta samu babban ci gaba.

"Wannan ita ce nasarar da jam'iyyarmu za ta samu. Gwamnan ya samar da zaman lafiya, bunkasa rayuwa da kuma shugabanci na gari, zamu samu yardar mutane."

KARANTA WANNAN: Gwamnan Ebonyi ya sha alwashin mayar da mutane 60,000 attajirai kafin ya sauka daga mulki

Dalilin da ya sa APC za ta samu nasara a zaben Ondo - Sanwo-Olu
Dalilin da ya sa APC za ta samu nasara a zaben Ondo - Sanwo-Olu
Asali: UGC

Ya bayyana cewa jam'iyyar APC za ta lashe zaben da zata kara tsakaninta da 'yan takarkaru 16 da suka fito daga wasu jam'iyyun.

Ya kuma kalubalanci gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Olusegun Mimiko.

"Al'ummar Ondo ba su gamsu da mulkin gwamnatin Mimiko na shekaru 8 ba, taron tsintsiya babu shara, amma shi gwamna Akeredolu ya yi aiki sosai a shekaru hudunsa na farko.

"Ya kawo sauyi sosai a rayuwar al'umma musamman talakawa, 'yan tsaka tsakiya da kuma attajiran jihar. Hasalima, kokarinsa ne ma yasa bamu samu ciwon kai sosai yanzu ba."

Da aka tambayeshi sakonsa ga jam'iyyun hamayya, Mr Sanwo-Olu ya bukaci jam'iyyun da su kauracewa bata lokutansu a banza.

Sai dai ya ce babu wata jam'iyyar da APC za ta yi mata rikon sakainar kashi.

Duk da cewa jam'iyyu 16 ne za su yi takara a zaben, akwai dai manyan jam'iyyu guda 3 da suka fi daukar hankali. Sune Mr Akeredolu daga APC, Eyitayo Jegede daga PDP da kuma Agboola Ajayi daga ZLP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel