Katsina: An damke jami'in hukumar shiga da fice da shanun sata 164

Katsina: An damke jami'in hukumar shiga da fice da shanun sata 164

Hukumar yan sandan jihar Katsina a ranar Alhamis ta damke wani Insfekta na hukumar shiga da fice (Immigration) tare wasu biyar da shanun sata 164 a jihar.

Jami'in hukumar shiga da fice, Abubakar Shafiu, wanda aka bayyana a Katsina tare da abokan laifinsa, ya bayyanawa manema labarai cewa wadanda aka kama su tare: Mohammad Isah, Ibrahim Mohammed, Idris Mohammad, Usman Mohammed da Saidu Lawal, yan uwansa ne dake zaune a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Bayan haka, Shafiu wanda yayi ikirarin shi ma'aikacin sashen saye-saye ne a hukumar shiga da fice ya ce ya samu hutu a wajen aiki yanzu kuma ya fitar da motocin shanu daga Zamfara kafin aka kamasu.

Amma ya musanta zargin cewa shanun sata ne, ya ce kawai masu shanun ne ke kokarin kaisu Potiskum da Buni Yadi a jihar Yobe saboda hare-haren yan bindiga a jihar Zamfara.

Katsina: An damke jami'in hukumar shiga da fice da shanun sata 164
Katsina: An damke jami'in hukumar shiga da fice da shanun sata 164
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Buruji Kashamu ya janye kararsa da Adebutu kafin ya mutu inji Lauyansa

Kakakin hukumar yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da rahoton kuma yace an damkesu ne ranar Alhamis misalin karfe 1:30 na dare a Jibiya, jihar Katsina bayan labarin leken asirin hukumar yan sanda tare da na kwastam suka samu cewa ana tafiyar da shanun da ake zargin na sata ne kuma Shafi'u na raka su.

"Muna gudanar da bincike kan lamari; duk mun san ana satan shanu a Katsina da Zamfara, kuma musamman, mun san a Zurmi manyan barayin suke boyewa."

"Ba zamu gajiya ba, zamu cigaba da gudanar da bincike kan inda aka samo shanun kuma mu tabbatar da cewa duk wanda aka kama da kashi a gindi zai gurfana a kotu," Gambo Isa ya labutra.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel