El-Rufa'i ya yi martani kan janye gayyatar da NBA ta masa

El-Rufa'i ya yi martani kan janye gayyatar da NBA ta masa

Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i ya bayyana janye gayyatar da kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA, ta yi masa a matsayin mai jawabi a wurin taron ta da 'rungumar rashin adalci'.

NBA ta janye rungumar da ya yi wa El-Rufai ne bayan wasu daga cikin lauyoyin sun koka tare da nuna amincewar su.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun sa, Muyiwa Adeleke, ya fitar a madadinsa a ranar Alhamis, ya ce El-Rufai zai cigaba da yin tsokaci a kan batutuwan da ya ke ganin za su kawo cigaba a kasar duk da janye gayyatar.

El Rufai ya yi martani kan janye gayyatar da NBA ta masa
El Rufai ya yi martani kan janye gayyatar da NBA ta masa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda wata budurwa ta yi garkuwa da kanta domin samun kuɗi daga iyayenta

"Duk da cewa NBA ce ke da ikon zabar wanda zai yi jawabi a wurin taron ta, Malam El-Rufai yana son a sani cewa dama ba shi ya nemi a gayyace shi ba kuma janyewar ba za ta rage shi da komai ba," in ji sanarwar.

"Ga ƙungiyar da ya dace ta rika bawa adalci muhimmanci, abin mamaki ne yadda ta yanke hukunci a kan al'amarin ba tare da jin ta bakin bangarorin biyu ba. Yadda suka bari matsin lamba ya canja musu ra'ayi alama ce da nuna sun rungumi rashin adalci da rashin bin doka."

Gwamnan ya ce zai mayar da martani a kan bata masa suna da aka yi a lokacin da ya sace cikin takardar ƙorafin da aka shigar a kansa.

A cikin wata takardar ƙorafi, Koyinsola Akayi, shugaban kwamitin ƙwararru na taron na NBA, a ƙarƙashin wata ƙungiya mai suna 'Open Bar Initiative laywers' sun ce gwamnan ya musguna musu.

Kungiyar ta kuma ƙara da cewa an sha ambaton Kaduna a matsayin jiha mafi hatsari a Najeriya a shekarar 2020 kuma El-Rufai a lokuta da dama yana keta hakkokin ƴan Najeriya.

Sai dai El-Rufai ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai da dama domin magance matsalolin rashin tsaro a jihar.

"Shine gwamnan da ya samar wa sojoji sansanin dindindin a Kudancin Kaduna, abinda aka kwashe shekaru 40 ana nema. Shine gwamnan da ya kafa kwamitin samar da zaman lafiya ta ke ƙarfafawa mutune gwiwa su zauna lafiya da juna," in ji sanarwar.

Adeleke ya ce gwamnan zai cigaba da mayar da hankali a kan babban aikin da ke gabansa na kawo karshen rikice-rikicen jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel