Za a yi wa matar da ta kashe dan ta a Kano gwajin kwakwalwa

Za a yi wa matar da ta kashe dan ta a Kano gwajin kwakwalwa

Babban kotun Jihar Kano a ranar Laraba ya bada umurnin a kai wata mata, Saratu Yau asibitin kwakwalwa domin duba ta bayan ta kashe dan ta mai shekara biyar, Buhari Abubakar.

Matar mai shekaru 27 ta aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2018 a kauyen Sabon Birni da ke karamar hukumar Gwarzo na jihar Kano.

An gurfanar da Saratu ne a gaban kotun bisa tuhumar aikata laifin kisan kai a ranar Laraba.

Lauya mai shigar da kara, Mr Lamido Sorondinki, ya shaidawa kotu cewa Saratu ta aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Yunin 2018 a Sabon Birni, Gwarzo.

Za a yi wa matar da ta kashe dan ta a Kano gwajin kwakwalwa
Za a yi wa matar da ta kashe dan ta a Kano gwajin kwakwalwa
Asali: Twitter

Sorondinki ya ce Saratu ta yi wa dan ta mai shekaru 5 yankar rago ne wadda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.

A cewar mai shigar da karar, laifin da ta aikata ya ci karo da sashi na 221 na dokar Penal Code.

Wacce ake tuhumar ta amsa aikata laifin.

Alkalin kotun, Mai sharia Ibrahim Karaye, ya dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2020 lokacin an samu sakamakon gwajin da asibitin za su yi mata.

DUBA WANNAN: An nadi bidiyon ‘Yaran Magu’ suna neman toshiyar bakin N75m daga hannun ɗan kasuwa

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji Yan sandan jihar Kano sun ceto wani bawan Allah mai shekaru 55, Murtala Muhammad da mahaifinsa ya rufe shi a daki bayan daure masa kafa na tsawon shekaru 30.

Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.

An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali kamar yadda Sahara Reotrers ta ruwaito.

Muhammad ya ce ya yi farin ciki da aka cece shi daga halin da mahaifinsa ya jefa shi ciki.

Kwamared AA Haruna Ayagi, Shugaban Human Rights Network ya ce tun lokacin Muhammad yana da shekaru 25 a duniya aka rufe shi a gida aka daure kafarsa a jikin reshen itace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel