Buhari ya ware N13bn domin sabon tsarin 'yan sandan al'umma

Buhari ya ware N13bn domin sabon tsarin 'yan sandan al'umma

Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da kudi Naira Biliyan 13.3 domin fara kaddamar da sabon shirin yan sandan al'umma.

Wannan na dauke ne cikin wani rahoto da aka mika wa Majalisar Tattalin Arziki na Tarayya, NEC a ranar Alhamis da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman ta.

Kwamitin wucin gadi a kan tsaro da aikin yan sanda karkashin jagorancin Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi ce ta mika rahoton ga NEC.

Buhari ya ware N13bn domin sabon tsarin yan sandan al'umma
Buhari ya ware N13bn domin sabon tsarin yan sandan al'umma
Asali: Twitter

Da ya ke bayyana abubuwan da aka tatauna yayin taron da aka gudanar ta hanyar amfani da intanet, Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce kwamitin wucin gadin ta zauna a ranar 4 ga watan Agusta don bita kan karuwar tabarbarewar tsaro a kasar.

DUBA WANNAN: Kungiyar ISWAP ta yi garkuwa da mutane masu dimbin yawa a Borno

A cewarsa, shugabannin hukumomin tsaro da suka hada da Mai Bawa Shugaban Kasa shawara a kan tsaro, NSA, Sufeta Janar na Yan sanda, IGP, da Shugaban Tsaro na Kasa da Hukumar Yan Sandan Farin Kaya, DSS, duk sun gabatar da jawabai.

"Majalisar ta yanke shawarar cewa shugaban NGF, (Kungiyar gwamnonin Najeriya) da wasu gwamnonin biyu za su rika ganawa da sakataren gwamnatin tarayya, ministan kudi da sufeta janar na yan sanda domin tsara yadda za a yi amfani da kudin na kafa yan sandan alumma. Gwamnatin tarayya ta riga ta ware Naira biliyan 13 domin aiki."

Ya kuma ce taron da lura cewa ofishin mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro , NSA, ba ta samun kudaden da ya dace a bata domin gudanar da ayyukan ta yadda suka kamata.

"Gwamnonin jihohi na kashe makuden kudade a kan tsaro saboda haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara samar da kudade domin a kara a kan abinda jihohin ke bayarwa da wasu abubuwa," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel