Borno ta karba mutum 94 da suka yi nasarar tserowa daga hannun Boko Haram

Borno ta karba mutum 94 da suka yi nasarar tserowa daga hannun Boko Haram

Gwamnatin jihar Borno ta ce ta karba mutum 94 da suka hada da kananan yara 40, wadanda suka tsero daga hannun 'yan Boko Haram.

Wakilai daga jami'an gwamnatin jihar sun karba 'yan Najeriya daga jamhuriyar Chadi, jaridar The Cable ta wallafa.

A wata takarda da ta fito daga kakakin gwamnan jihar, Isa Gusau, ya ce, wadanda suka tsero sun hada da maza 37, mata 17 da kananan yara 40.

Jami'an tsaro na hadin guiwa ne suka cetosu bayan artabun da suka yi da mayakan ta'addancin.

Ya ce kwamandan MNJTF, Ibrahim Yusuf, ya mika wadanda ake ceto ga gwamnatin jihar.

Isa ya ce, "wasu daga cikinsu da kansu suka mika kansu ga jami'an tsaron yayin da matan da kananan yara cetosu aka yi."

Kamar yadda takardar tace, wasu daga cikin wadanda aka ceto mika kansu suka yi, don haka dole a bincika tare da gano alakar da ke tsakaninsu da mayakan ta'addancin.

"Akwai manyan alamu da ke nuna cewa ana samun nasara wurin yakar ta'addancin. Nasara ba ita bace yadda suke mika kansu ko yawan wadanda ake kashe ba ko kuma raguwar yawan jama'ar da ke shiga cikinsu," Yusuf yace.

Borno ta karba mutum 94 da suka yi nasarar tserowa daga hannun Boko Haram
Borno ta karba mutum 94 da suka yi nasarar tserowa daga hannun Boko Haram. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita

“Nasara ita ce yadda jami'an tsaron suka dage suna aiki tukuru a kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya. Yadda ake tsananta musu ne nasara."

Kwamishinan shari'a na jihar Borno, Kakashehu Lawan, ya karba wadanda aka ceto a madadin gwamnatin jihar. Ya ce za a duba tare da mayar da su cikin jama'a.

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun kawar da harin yan ta'addan Boko Haram da ISWAP suka kai cikin garin Kukawa, a jihar Borno ranar Talata.

Hukumar ta yi bayani ranar Alhamis cewa jami'an sun samu nasarar hallaka yan ta'addan takwas amma anyi rashin jaruman soji uku kuma wasu sun jikkata.

A jawabin da jagoran sashen yada labaran hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Eneche, ya saki, yace, "Yayin artabun, an hallaka yan ta'addan Boko Haram 8, kuma wasu cikinsu sun tsira da raunukan harsashi."

Ya kara da cewa, "Amma abin takaici, an yi mumunan jikkata sojoji uku kuma daga baya suka kwanta dama a asibitin Soji dake Kukawa."

Ya ce wasu Soji biyu sun jikkata kuma suna samun kula yanzu haka a asibitin Soji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel