Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsari a wando

Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsari a wando

- Yan sanda sun samu gawar Autumn Hallow, yar shekara takwas ranar Alhamis bayan kiran gaggawa ta 911

- Kishiyar mahaifiyarta, Sarah Hallow, ta ce ita ma kawai ganinta tayi cikin bayi fuskarta a durkufe.

- Bincike ya nuna cewa ta mutu tun kafin zuwan jami'an tsaro

Wani mutumi da amaryarsa sun shiga hannun hukuma a birnin Minnesota, kasar Amurka bayan kisan diyar uwarigida mai shekaru takwas da haihuwa, Autumn, bayan daureta cikin jakar leda don ta yi fitsari a wando.

An tsinci gawan yarinyar cikin randan wanka misalin karfe 3:45 na rana yayinda aka kira jami'an yan sanda, Daily Mail ta ruwaito.

A cewar ofishin yan sandan Sherburne County, yayinda suka dira wajen sun samu kishiyar mahaifiyar yarinyar, Sarah Hallow, tana kokarin farfado da yarinyar.

Duk yunkurin da aka yi na ceton rayuwarta ya ci tura yayinda aka sanar da mutuwarta a lokacin.

Masu bincike sun bayyana cewa da yiwuwan ta dade da mutuwa kafin a kira yan sanda, saboda yanayin yadda aka samu jikinta.

Tuni an garkame Uban yarinyar, Brett Hallow da amaryarsa, Sarah Hallow kuma an tuhumesu da laifin kisan kai, a cewar Twin Cities Pioneer Press.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun ki fada mani inda su ka kai Mai gidana – Uwargidar Mubarak Bala

Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsarin kwance
Uba da Amaryarsa sun kashe diyar uwargida don tayi fitsarin kwance
Asali: Facebook

A wani labari na daban, Jami'an yan sanda a jihar Kano sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.

Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.

Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi.

Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel