Gwamnan Ebonyi ya sha alwashin mayar da mutane 60,000 attajirai kafin ya sauka daga mulki
- Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi ya ce zai tsamo 'yan Ebonyi 60,000 daga kangin talauci zuwa attajirai
- David Umahi ya ce zai yi hakan ne ta hanyar shirye shiryen bada tallafin makudan kudade ga 'yan jihar
- Umahi ya bayyana hakan ta bakin kwamishiniyar ma'aikatar bunkasa rayuwa da sa ido, Mrs Ann Aligwe
Gwamnan jihar Ebonyi David Umahi a ranar Laraba ya ce zai tsamo 'yan Ebonyi 60,000 daga kangin talauci zuwa attajirai, ta hanyar shirye shiryen bunkasa rayuwarsu.
Ya ce zai tabbatar ya cika wannan kudurin nasa kafin karewar wa'adin mulkinsa a 2023.
Umahi ya bayyana hakan ta bakin kwamishiniyar ma'aikatar bunkasa rayuwa da sa ido, Mrs Ann Aligwe a yayin taya murnar ranar aikin jin kai na duniya a garin Abakaliki.
A cewar Aligwe, wadanda zasu ci gajiyar shirin za a zabo su ne daga kananan hukumomi 13 na jihar.
"Gwamnanmu Engr. David Umahi na shirin mayar da mutane 60,000 attajirai ta hanyar shirye shiryen tallafi da gwamnatin ke kawowa.
"Zamu bunkasa kasuwancin cikin gida da waje daga nan zuwa watan Fabrerun shekara mai zuwa. A shirin shigo da kaya da fita dasu, za a zabi mutane 3 daga kowacce karamar hukuma.
KARANTA WANNAN: Rundunar soji ta fara dibar sabbin soji - Yadda za ka shiga

Asali: Facebook
"Za a turasu China, Turkey da Dubai don sayowa gwamnatin Ebonyi kaya.
"Makon da ya gabata gwamna ya amince da fitar da miliyan dari da talatin, a rabawa mutane 130 karkashin ofishin SA, kanana da matsakaitun 'yan kasuwa.
"Gwamnan ya kuma amince a fitar da wata miliyan 130, a ba kwamishinan kasuwanci da masana'antu, domin a rabawa jama'a tallafi.
"Haka zalika an sake fitar da wata miliyan 130 domin a rabawa 'yan kasuwa ta hannun kwamishinan bunkasa kasuwanci.
"A hannu daya kwamishinan bunkasa kasuwanni zai raba miliyan 200 ga 'yan kasuwa mata. Dukanin wadannan kudaden an basu don su rarraba.
"A karkashin ma'aikata ta, gwamnan ya amince a bamu miliyan 450 domin rabawa manyan kamfanoni uku da ke shiyyoyin jihar. Za a ba kowanne kamfani miliyan 150."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng