Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC

- Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Joseph Chiedu Ugbo a matsayin shugaban NDPHC

- Buhari ya kuma amince da sabunta naɗin Babayo Shehu da Ifeoluwa Oyedele a matsayin manyan direktoci a NDPHC

- Har wa yau, Shugaban ƙasar ya bada umurnin sake naɗa sabbin direktoci uku a hukumar domin fadada da inganta ayyuka

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sabunta naɗin Mista Joseph Chiedu Ugbo a matsayin shugaban hukumar samar da lantarki na yankin Niger Delta (NDPHC).

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman a fanin kafafen watsa labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Mr Laolu Akande ya fitar a ranar Alhamis.

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC
Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

Sanarwar ta kuma ambaci haɗin Mr Babayo Shehu da Ifeoluwa Oyedele a matsayin manyan direktocin hukumar na wa'adin shekaru hudu.

"Wannan sabunta naɗin zai fara aiki ne daga ranar 25 ga watan Agustan 2020 na tsawon shekaru huɗu (4).

"An kuma amince da nadin wasu ƙarin manyan direktoci uku a hukumar domin inganta aiki da fadada aikin kamfanin," a cewar sanarwar.

A wani rahoton, Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta amince da kashe N3.9bn domin kammala aikin ginin sakatariyar tarayya a jihohin Anambra, Bayelsa, Nasarawa, Osun, da Zamfara.

Kazalika, FEC ta amince da kashe N1.5bn domin sake inganta haka Dam din Usuma da ke karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan aiyuka da gidaje, Babatunde Fashola, da takwaransa na birnin tarayya (FCT), Muhammad Bello, sun tabbatar da hakan yayin ganawarsu da manema labarai bayan kammala taron FEC.

Shugaba Buhari ne ya jagoranci taron FEC na Laraba, da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo ta intanet a fadar shugaban kasa.

Mista Fashola ya bayyana cewa an fara bayar da kwangilar aikin gina sakatariyar a kan kudi N13.5bn a shekarar 2011, inda ya kara da cewa an kara ware N3.9bn domin kammala aikin gaba daya a jihohin biyar wanda zai lashe jimillar kudi N17.4bn.

Ministan ya kara da cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta samarwa dukkan ma'aikatanta ofisoshin aiki a duk jihohin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel