Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun sace mutane 5

Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun sace mutane 5

- Yan bindiga a daren ranar Laraba sun shiga jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da mutane biyar a garin

- Yan ta'addan sun shiga garin ne haye a babura, inda suka bude wuta kan mai uwa da wani, suna kona gidaje da rumbunan abinci

- Jihar Katsina ta kasance tana fama da hare haren 'yan ta'adda

Yan bindiga a daren ranar Laraba sun shiga garin Daudawa, karamar hukumar Faskari, jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da mutane biyar a garin.

Wani mazaunin yankin, Mallam Nasiru ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa 'yan bindigar sun kuma yi awon gaba da dabbobi da kayan abincinsu masu yawa.

Ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun shiga garin ne haye a babura, inda suka bude wuta kan mai uwa da wani, suna kona gidaje da rumbunan abinci.

Jihar Katsina ta kasance tana fama da hare haren 'yan ta'adda a 'yan tsakanin nan, wanda ya haddasa asarar rayuka da kuma tilasta daruruwan jama'a barin garuruwansu.

KARANTA WANNAN: Buhari ya shiga ganawa da shuwagabannin ECOWAS kan rikicin Mali

Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun sace mutane 5
Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun sace mutane 5
Asali: Facebook

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawa tare da sauran shuwagabannin kungiyar kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta, 2020.

Ganawar tana gudana ne ta kafar yanar gizo, kamar yadda shafin fadar shugaban kasa ta wallafa a shafinta na Twitter.

Shuwagabannin ECOWAS, suna wannan ganawar ne a ci gaba da neman hanyoyin dai daita rikicin siyasa da ya barke a kasar Mali, wanda ya kai ga anyi juyin mulki a ranar Talata.

A ranar Laraba ne ECOWAS ta fitar da sanarwar dakatar da kasar Mali daga cikin ayyukan kungiyar tare da umurtar kasashen dake kungiyar su rufe iyakokin kasashensu da Mali.

A ranar Talata, sojojin hamayya suka cafke shugaban kasa Keita da Firam Minista Boubou Cisse, bayan makonni na tashin hankali a kasar da ya fara daga ranar 10 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel