Soji sun kashe yan Boko Haram 8, an yi rashin jaruman Soji 3 a garin Kukawa

Soji sun kashe yan Boko Haram 8, an yi rashin jaruman Soji 3 a garin Kukawa

Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun kawar da harin yan ta'addan Boko Haram da ISWAP suka kai cikin garin Kukawa, a jihar Borno ranar Talata.

Hukumar ta yi bayani ranar Alhamis cewa jami'an sun samu nasarar hallaka yan ta'addan takwas amma anyi rashin jaruman soji uku kuma wasu sun jikkata.

A jawabin da jagoran sashen yada labaran hedkwatan tsaro, Manjo Janar John Eneche, ya saki, yace, "Yayin artabun, an hallaka yan ta'addan Boko Haram 8, kuma wasu cikinsu sun tsira da raunukan harsashi."

Ya kara da cewa, "Amma abin takaici, an yi mumunan jikkata sojoji uku kuma daga baya suka kwanta dama a asibitin Soji dake Kukawa."

Ya ce wasu Soji biyu sun jikkata kuma suna samun kula yanzu haka a asibitin Soji.

Ya bayyana cewa a ranar 29 ga yuli, 2020, gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya kaddamar da bude titin Munguno zuwa Kukawa kuma daga nan mutane suka fara komawa.

Ya ce yan ta'addan sun kai harin gayya ne domin mayar da hannun agogon nasarorin da gwamnatin jihar ta samu baya wajen; samar da zaman lafiya, gayra gine-gine da mayar da mutane muhallansu na asali.

Ya ce komai ya yi sauki yanzu a Kukawa kuma Soji sun mamaye garin.

Soji sun kashe yan Boko Haram 8, an yi rashin jaruman Soji 3 a garin Kukawa
Soji sun kashe yan Boko Haram 8, an yi rashin jaruman Soji 3 a garin Kukawa
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel