Mamman Daura yana nan lafiyarsa ƙalau - Fadar Gwamnati

Mamman Daura yana nan lafiyarsa ƙalau - Fadar Gwamnati

- Wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton cewa ɗan uwan Shugaba Buhari, Mamman Daura ya fita ƙasar waje neman magani

- Majiyar ta ce Mamman Daura ya tafi birnin Landan ne domin wasu harkokin kasuwanci amma lafiyarsa ƙalau

- Majiyar ta bukaci ƴan Najeriya su yi watsi da jita jitar domin babu gaskiya cikin lamarin inda ta ce zai dawo da zarar ya kammala abinda ya kai shi

Fadar shugaban kasa a jiya Laraba ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ɗan uwan Shugaba Buhari, Malam Mamman Daura ya fita kasar waje neman lafiya, ta ce lafiyar shi ƙalau.

Ta yi martani ne ga wani rahoto da wata kafar watsa labarai na intanet ta wallafa na ikirarin cewa an shilla da Mamman Daura zuwa ƙasar Ingila domin yi masa magani game da wata rashin lafiya da ya ke fama da shi.

Mamman Daura yana nan lafiyarsa ƙalau - Fadar Gwamnati
Mamman Daura yana nan lafiyarsa ƙalau - Fadar Gwamnati
Asali: UGC

Wata ƙwakwarar majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida wa jaridar Leadership a daren jiya Laraba cewa Daura ya tafi Landon ne domin gudanar da wasu buƙatunsa na kasuwanci.

DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali

Majiyar da ya nemi a sakayya sunansa saboda ba a bashi izinin yin tsokaci a kan lamarin ba ya ce Mamman Daura yana cikin ƙoshin lafiya.

"Zai dawo idan ya kammala harkokin kasuwancin da suka saka shi balaguro zuwa Birtaniya.

"Mamman Daura lafiyarsa ƙalau. Jita-jitar cewa bashi da lafiya ne yasa aka tafi da shi ƙasar waje ba gaskiya bane. Ya tafi Landon ne domin kasuwanci da ya daɗe yana shiri. Da zarar ya gama zai dawo," kamar yadda aka sanar da majiyar Legit.ng

Majiyar da ya yi iƙirarin cewa ya yi magana da Mamman Daura a baya bayan nan ya ce ," labarin ƙarya ce tsantsagwaron ta", ya kuma bukaci ƴan Najeriya su yi watsi da labarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel