Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata

Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata

- Wani bidiyon sojojin Najeriya suna lakadawa wani tsoho mugun duka ya karade kafafen sada zumuntar zamani

- A bidiyon, an ga zakakuran sojojin suna dukan tsohon tare da tirsasa shi shiga kwata yayin da jama'a suka zagayesu suna kallo

- Daya daga cikin masu kallon ya kasa jurewa inda yake tunatar da sojojin cewa tsoho ne mutumin amma basu ko bi ta kansa ba

Wani bidyon sojojin Najeriya da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani ya janyo cece-kuce. Jama'a da tarin yawa sun bayyana firgicinsu a kan lamarin da ke faruwa a bidiyon.

Wasu sojojin Najeriya ne suka lakadawa wani tsoho duka tare da tirsasa shi shiga cikin kwata.

A cikin bidyon, an ga jama'a sun taru suna kallo cike da alhinin lamarin, jaridar The Nation Community ta wallafa.

An ji daya daga cikin masu kallon yana ihu tare da cewa "tsoho ne fa, tsoho ne fa" a cikin harshen turanci.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani na Facebook mai suna Ubi Franklin, ya wallafa bidiyon.

Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata
Bidiyon sojojin Najeriya suna yi wa tsoho duka tare da saka shi shiga kwata. Hoto daga The Guardian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita

Ga bidiyon a kasa:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel