Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita

Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta mika korafi gaban rundunar 'yan sandan jihar Legas a kan yunkurin wani dan kasar Faransa na yin fyade ga wata matar aure 'yar Najeriya da ke aiki a gidansa.

Kungiyar rajin kare hakkin dan Adam din ta mika korafin ne a madadin matar mai suna Mariam Ukpoji, wacce take aiki a gidan wani mutum mai suna Gueho Benoit dan kasar Faransa.

Kamar yadda koken ya bayyana, mijin matar yana aiki a matsayin direba da kamfanin Bourbon Inter Oil Nigerian limited da ke Ikoyi a jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Ita kuwa matarsa mai suna Mariam, tana aikin cikin gida ne kuma dukkansu kamfanin ne ya basu wurin zaman.

Sun ce Benoit ya kira matar kuma ya fara yunkurin lalata da ita amma ta jajirce inda ta hana shi tare da ihun neman taimako.

Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita
Matar aure 'yar Najeriya ta sanar da yadda ubangidanta dan Faransa ya yi yunkurin lalata da ita
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita

"Ya ja matar cikin dakinsa a kan cewa zai kai karar halayyar mijinta gareta, Benoit ya ci zarafinta ta hanyar yunkurin lalata da ita.

"Rashin yarda da shi ne yasa ya dinga dukanta har ya yi mata tsirara tare da zaginta.

"Matar auren ta dinga ihun neman taimako ta yadda jami'an tsaron da ke aiki ranar da sauran jama'a suka balle kofar don cetonta.

"An kama shi tsirara yayin da matar auren take rabi tsirara," Kenpeacemaker Onojah, shugaban kungiyar ya bayyana.

Ya kara da cewa, bayan rokon da Benoit ya dinga yi, an sakesa amma kuma matar ta kai kara kamfanin man.

Shugaban kungiyar rajin kare hakkin dan Adam din, ya ce kungiyarsa na bukatar kamfanin da ya bada dan kasar Faransar.

Amma kuma, shugaban ya ce jami'an 'yan sanda bayan kwanaki kadan sun bayyana a gidan matar inda suka lallasa mata mugun duka tare da barazanar kasheta.

"Benoit ya bamu hakuri kuma ya dauka alkawarin biyan matar da mijinta N200,000.

"Babu tsagaitawa suka kai korafinsu gaban kamfanin Bourbon Inter Oil ta hannun mataimaki na musamman na manajan daraktan kamfanin.

"Ya tabbatar da cewa za a yi musu adalci kuma hukumar kamfanin ta fara bincike don sanin yadda za ta shiga lamarin," ya kara da cewa.

Onojah ya yi kira ga kwamishinan 'yan sandan Najeriya da ya gaggauta fara bincike a kan lamarin tare da tabbatar da cewa an yi adalci.

'Yan sandan da suka shiga lamarin tare da yin barna kuwa a zakulosu tare da ladabtar da su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel