Da dumi-dumi: Sabbin mutum 593 sun kamu da cutar korona a Najeriya
Hukumar Takaita Yaduwar Cututtuka a Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 593 a fadin Najeriya a yau.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:29 na daren ranar Laraba 19 ga Agusta, 2020.
A cikin sanarwar da NCDC ta a shafinta na Twitter, ta bayyana yadda wadanda suka kamu a jihohin Najeriya kamar haka:

Asali: Twitter
Plateau-186
Lagos-172
FCT-62
Oyo-27
Delta-25
Rivers-20
DUBA WANNAN: Kwanel Assimi Goita ya naɗa kansa shugaban ƙasa na mulkin soja a Mali
Ondo-19
Edo-18
Kaduna-17
Enugu-12
Akwa Ibom-10
Ogun-7
Abia-6
Gombe-6
Kano-3
Osun-3
Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Laraba 19 ga Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 50,488 .
An sallami mutum 37,304 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 985.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng