UCL: Bayern Munich ta fito wasan karshe a gasar zakarun nahiyar Turai
Kungiyar kwallon kafa ta Byern Munich da ke kasar Jamus ta samu zuwa wasan zagaye na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai bayan ta lallasa kungiyar Lyon ta kasar Faransa da ci 3 - 0.
Dan wasan kungiyar Bayern Munich, Serge Gnabry, ya samu damar zura kwallo biyu a wasan kafin daga bisani dan wasan gaba na kungiyar, Robert Lewandowski, ya zura kwallo ta uku a minti na 55 da take wasa.
Hakan na nufin cewa kungiyar Munich za ta kara da kungiyar Paris Saint German (PSG) ta kasar Faransa a wasan karshe da za a buga a ranar Lahadi, 23 ga watan Agusta.
Kungiyar Munich ta samu nasarar lallasa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ci 8 - 2 a wasan kusa da na karshe da suka buga da yammacin ranar Litinin, 17 ga watan Agusta.
Kazalika, kungiay PSG ta samu nasarar lallasa kungiyar Leipzig ta kasar Jamus da ci 3 - 0 a wasan da suka fafata da yammacin ranar Laraba.
Wanna shine karo na farko da kungiyar PSG ta samu damar fitowa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
A wani labarin mai nasaba wasanni da Legit.g Hausa ta wallafa da yammacin ranar Talata, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da daukan tsohon dan wasanta na tsakiya, Ronald Koeman, a matsayin sabon mai horar da 'yan wasanta.
DUBA WANNAN: Yadda Abacha ya kamani ya daure a 1995 bayan na ki daukan shawarar Carrington - Obasanjo
Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Josep Maria Bartomeu, ne ya sanar da hakan a jawabin da ya gabatar ranar Talata.
"Koeman zai kasance sabon kociyan kungiyar Barca daga zangon wasa na gaba," a cewar Bartomeu a sanarwarsa da aka nuna a gidan talabijin na kungiyar Barcelona.
Koeman, kociyan kungiyar kwallon kafa ta kasar Netherlands tun shekarar 2018, zai maye gurbin Quieque Setien, tsohon kociyan da aka kora bayan kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus ta lallasa Barcelona da ci 8 - 2 a gasar zakarun Turai.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da fatattakar Setien a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng