Tun da an kawar da shugaba Keita, zan koma Limanci na a Masallaci - Imam Mahmoud

Tun da an kawar da shugaba Keita, zan koma Limanci na a Masallaci - Imam Mahmoud

Daya daga cikin jagororin adawa a kasar Mali kuma Malamin addini, Imam Mahmoud Dicko, ya bayyana cewa zai koma aikinsa na limanci tun da burinsu na tunbuke shugaba Ibrahim Kaita ya cika, sashen Hausa na BBC ta ruwaito.

Imam Mahmoud Dicko na daga cikin manyan da suka rika jagorantan zanga-zanga a Mali har aka tunbuke shugaban kasa da gwamnatinsa.

Imam Dicko ya kasance kan gaba wurin zanga-zanga, inda ya rinƙa jagorantar sama da mutum dubu goma a titunan Bamako babban birnin ƙasar.

Tun da an kawar da shugaba Keita, zan koma Limanci a Masallaci - Imam Mahmoud
Tun da an kawar da shugaba Keita, zan koma Limanci a Masallaci - Imam Mahmoud
Asali: UGC

A jiya Talata, Sojoji a kasar Mali sun damke shugaban kasa, Ibrahim Boubacar Keita, da firam Ministansa, Boubou Cisse, daya daga cikin shugabannin Sojin ya bayyana.

"Muna masu fada muku cewa shugaban kasa da Firam Minista na hannunmu" Daya daga cikin Sojin ya bayyanawa AFP.

Ya bayyana cewa an damke su biyun nan a gidan shugaban kasan dake birnin kasar, Bamako.

Gabanin damke shugaban kasan a yau Talata, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, wanda shine wakilin ECOWAS da aka tura sulhunta rikicin Mali, ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari.

Ya bayyanawa Buhari cewa kungiyar adawa a kasar Mali, M5, ta doge kan bakanta cewa sai shugaba Keita ya yi murabus.

Za ku tuna cewa a watan Yuli, shugaba Buhari da wasu shugabannin ECOWAS sun kai ziyara kasar Mali domin sulhunta bangarori biyu amma ganawarsu da shugaban hamayya, Imam Dicko, ya kare a baran-baran.

KU KARANTA: WAEC: Karin Dalibai 7 sun kamu da Korona a jihar Gombe

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel