Da duminsa: An fitar da Mamman Daura kasar waje don ganin Likita

Da duminsa: An fitar da Mamman Daura kasar waje don ganin Likita

An fita da dan'uwan shugaba Muhammadu Buhari kuma amininsa, Alhaji Mamman Daura, kasar Birtaniya don ganin Likita bisa rashin lafiyan da yake fama, Sahara Reporter ta ruwaito.

A cewar rahoto, an fitar da Mamman Daura ne yau Laraba cikin jirgi bayan ya fara fama da matsalar numfashi da wasu alamomin kamuwa da cutar Korona tun ranar Juma'a.

A cewar wasu, tsohon dan jaridan kuma babban aminin Buharin yana fama matsalar koda kuma ya kan ziyarci Turai don ganin Likita.

Da duminsa: An fitar da Mamman Daura kasar waje don ganin Likita
Da duminsa: An fitar da Mamman Daura kasar waje don ganin Likita
Asali: Twitter

A baya-bayan nan, Mallam Mamman Daura, ya yi magana kan kabilar da ya kamata a baiwa kujeran shugaban kasa.

A hirar da yayi da BBC Hausa, Mamman Daura ya ce bai kamata a yi amfani da yanki ko kabilar mutum don zabensi a 2023 ba. Kawai a duba cancanta.

Hakan ya janyo masa suka daga bangarori daban-daban inda suka ce kawai a cigaba da tsarin kama-kama.

Kungiyoyi irinsu Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo, Afenifere da South-South Elders’ Forum ta mutanen Arewa, Ibo, Yarbawa, Neja-Delta sun yi magana.

A hira da kungiyoyin su ka yi da jaridar a mabanbantan lokaci, sun nuna ba su goyon bayan kiran da Mamman Daura ya ke yi. Sai dai kungiyar ACF ta manyan Arewa ta ce dattijon ya yi gaskiya.

Shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, ya yi magana ta bakin hadiminsa, Emeka Attamah, ya na mai cewa akwai son rai a kalaman da ‘danuwan shugaban kasar ya yi.

Nnia Nwodo ya tunawa Mamman Daura cewa an fatattaki Goodluck Jonathan daga mulki a 2015 ne saboda mutanen yankin Arewa su na ganin cewa lokacinsu ne da za su yi mulkin kasar.

tsohon sakataren kungiyar Arewa ACF, Anthony Sani, yayi cewa ba a baiwa shugaba Buhari mulki ba don yana dan Arewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel