WAEC: Karin Dalibai 7 sun kamu da Korona a jihar Gombe

WAEC: Karin Dalibai 7 sun kamu da Korona a jihar Gombe

Kwamishinan ilimin jihar Gombe, Dakta Habu Dahiru, a ranar Laraba, ya ce karin dalibai mata 7 na makarantar sakandaren GGSS Doma, sun kamu da cutar Korona.

Adadin daliban da suka kamu da cutar daga fara jarabawar ranar Litinin ya kai takwas, Punch ta ruwaito.

A baya, rahoto ya nuna cewa wani dalibin jihar ya kamu da cutar kuma yana zana jarabawarsa daga cibiyar killace masu cutar.

Kwamishanan ilimin yayinda ya ziyarcu dalibin ya bayyana cewa ma'aikatarsa tare da hadin gwiwan kwamitin yaki da COVID-19 ta gudanar da gwajin Korona 1,100.

Yace: "Mun fi mayar da hankali kan daliban da suka dawo daga jihohi masu adadin cutar Korona mai yawa irin Kaduna, Kano, Yobe da Legas. Kawo yanzu, mun gwada mutane 1,100. Daga ciki aka samu mutum daya dalibin makarantar sakandaren kimiya GSSS."

"Da wuri aka garzaya da shi kuma aka killaceshi. Ya rubuta jarabawarsa ta farko - Lissafi - kuma yana rububa ilmin noma yau."

"Mun san ba zai ji dadi ba idan muka hanashi rubuta jarabawar."

WAEC: Karin Dalibai 7 sun kamu da Korona a jihar Gombe
WAEC: Karin Dalibai 7 sun kamu da Korona a jihar Gombe
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matasa sun kaiwa dan Fulani hari, sun sace masa shanu 28, sun illata 7

A bangare guda, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada izinin daliban sakandare da ke babban ajin karshe wato ss3 da karamin ajin karshe jss3 su dawo makaranta su rubuta jarrabawar fita wato SSCE.

Biyo bayan matakin da gwamnatin tarayyar da dauka, jihohin Najeriya su ma sun bi sahun bude makarantun domin daliban su rubuta jarrabawar fitan.

Sai dai kafin a bude makarantun, gwamnatin tarayya da maaikatan lafiya da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar korona duk sun bayar da kaidoji da makarantun za su bi don kiyaye lafiyar dalibai da malamansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel