Matasa sun kaiwa dan Fulani hari, sun sace masa shanu 28, sun illata 7

Matasa sun kaiwa dan Fulani hari, sun sace masa shanu 28, sun illata 7

Wasu matasa yan bindiga sun kaiwa wani Fulani Makiyayi hari har gidansa a garin Ankpa, jihar Kogi, inda suka kashe masa shanu 7 kuma sukayi awon gaba da 28.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya tattaro a Lokoja cewa yan bindigan sun dira gidan makiyayin dake unguwar Ogodo dake Ankpa ranar 30 ga Yuli kuma suka koma ranar 16 ga Agusta, 2020.

Makiyayin mai suna, Malam Lawal Ahmadu, a jawabinsa ya bayyana cewa matasan, rike da bindigogi, wukake da wasu muggan makamai, sun fara dira gidan ne ranar 30 ga Yuli kuma sukayi awon gaba da manyan shanu 9.

Ahmadu yace sun kara dawowa ranar 16 ga Agusta inda suka kwashe masa shanu 16 kuma suka illata wasu shanu 7.

Ya ce matasan sun dira gidansa ne cikin baburan Keke Napep da akfi sani da 'a daidaita sahu' kuma suka yanka shanayen a gabansa, sukayi tafi da naman.

A cewarsa, biyu cikin shanu 7 da suka harba sun mutu daga baya.

Ya ce shanu biyar kawai suka rage masa yanzu, kuma ya kai kara ga hukumar yan sanda, hukumar tsaron sa kai, shugabannin karamar hukumar da kungiyar Miyetti Allah.

Ya jaddada cewa iya dukiyar da ya mallaka kenan kuma matasan sun raba shi da su. Ya yi kira ga jama'a da gwamnati su kawo masa dauki.

Matasa sun kaiwa dan Fulani hari, sun sace masa shanu 28, sun illata 7
Matasa sun kaiwa dan Fulani hari, sun sace masa shanu 28, sun illata 7
Asali: UGC

Yayinda aka tuntubi sakataren kungiyar Miyetti Allah na jihar Kogi, Abubakar Adamu, ya ce an kai kara ofishin yan sanda da gwamnatin jihar.

Adamu ya ce an tura sakonni ga gwamnatin jihar domin biyan kudin diyya ga makiyayin saboda tabbatar da zaman lafiya cikin al'ummar jihar.

Ya bukaci yan sanda su zakulo matasan da suka aikata wannan aikin assha kuma su dakile tashin hankalin da hakan ya janyo cikin al'ummar Fulani.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP William Aya, wanda ya tabbatar da aukuwan hakan ya ce an damke mutane uku da ake zargi suna da hannu.

A cewarsa, kwamishanan yan sandan jihar, MIsta Ayube Ede, ya bada umurnin tura yan sanda wajen domin dakile yiwuwar sake kawowa Fulani hari.

Ya yi kira da Fulanin jihar kada su yi ramuwar gayya, ya bukacesu su bari yan sanda suyi aikinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel