Boko Haram sun jigata, ba su iya yakar soji na minti 5 - Rundunar soji

Boko Haram sun jigata, ba su iya yakar soji na minti 5 - Rundunar soji

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa mayakan ta'addancin Boko Haram sun jigata, basu da horo kuma ba su iya yakar jami'an tsaro su wuce minti biyar.

Wannan na zuwa ne a yayin da rundunar ke tunkahon mallakar zakakuran dakaru da kuma kayan aiki wanda ake tsare rayukan 'yan Najeriya.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, sojin Najeriya sun tsananta wurin kokarin ganin bayan 'yan ta'addan da suka wuce shekaru goma a jihar Borno.

Bayan tsananta wa 'yan ta'addan da dakarun sojin suka yi, manyan birane biyu da 'yan ta'addan suka kwace sun samu 'yanci, duk da ana ci gaba da samun hari da tashin bama-bamai a yankin.

A yayin da rundunar sojin take wannan tunkahon, ta yi wallafar a ranar Laraba a shafinta na Twitter, inda rundunar sojin ta ce jami'anta ba tsararrakin 'yan ta'addan bane.

Amma kuma sai dai ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani sun kalubalanci wannan ikirarin inda suka tuna yadda har yanzu 'yan ta'addan ke cin karensu babu babbaka a arewa.

Boko Haram sun jigata, ba su iya yakar soji na minti 5 - Rundunar soji
Boko Haram sun jigata, ba su iya yakar soji na minti 5 - Rundunar soji. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan kungiyar ta'addanci ta Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ne sun sace daruruwan mutane sunyi garkuwa da su a jihar Borno kamar yadda AFP ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan masu alaka da kungiyar, a daren jiya Talata sun kai hari a Kukawa da ke Tafkin Chadi inda suka sace mutane masu yawa da suka dawo gidajensu bayan shafe shakaru biyu a sansanin yan gudun hijira a cewar Babakura Kolo, shugaban yan sa kai na yankin.

A watan Yuni, a kalla sojoji 20 da farar hula fiye da 40 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wasu hare hare biyu da 'yan kungiyar suka kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika, yan kungiyar ta'addancin sun kashe a kalla mutum 81 a wani hari da suka kai a wani kauye da ke karamar hukumar Gobiyo a jihar Borno a watannin baya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel