Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita

Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita

Wata kotun Majistare da ke zama a Ikeja a ranar Laraba, ta bada umarnin tsare wani saurayi mai shekaru 37 a gidan gyaran hali da ke Kirikiri a jihar Legas.

Saurayin mai suna Abdulmalik, ana zarginsa ne da cin zarafin karamar yarinya mai shekaru hudu a duniya, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Alkalin kotun, Peter Nwaka, ya bai wa 'yan sandan umarnin mika takardun shari'ar gaban ofishin gurfanarwa na jihar Legas don shawara tunda bai saurari rokon da Malik ke yi ba.

Nwaka ya dage sauraron karar har zuwa ranar 29 ga watan Satumban 2020 don ci gaba.

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, ASP Benson Emuerhi, ya zargi Malik da aikata laifin a ranar 26 ga watan Fabrairu a gidansa.

Dan sandan ya bayyana cewa, Malik wanda ke zama a gida mai lamba 9, titin Olusegun Opaleye, fadar Ago, da ke Legas, ya ci zarafin karamar yarinyar.

Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita
Yadda matashi ya saka karamar yarinya a cinyarsa, ya dinga lalata da ita. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku

Emuerhi ya ce, wanda ake karar ya dora yarinyar a cinyarsa kuma ya yi lalata da ita. Ya ce an kai karar lamarin ofishin 'yan sanda da ke Ago.

Laifin ya ci karo da tanadin sashi na 261 na dokokin manyan laifuka na jihar Legas na 2015, wanda ya tanadi hukuncin daurin rai da rai.

A wani labari na daban, wani matukin motar haya mai shekaru 43 mai suna Idris Azeez, ya sanar da wata kotun gargajiya da ke Ile-Tuntun a Ibadan jihar Oyo, cewa matarsa mai suna Morenikeji ta bayyana masa kwartonta a matsayin babban yayanta.

Morenikeji ta kai korafi gaban kotun inda take bukatar a raba aurensu saboda Azeez ba shi da kula a matsayinsa na mijinta, kuma yana dukanta ba tare da dalili ba.

Ta bada labarin yadda ta taba karbar bashin banki domin fara sana'a amma Azeez ya handame tare da yin watanda da shi. Amma a yayin martani, Azeez ya ce Morenikeji na sane da cewa yana fuskantar wasu kalubale.

Ya ce, "Ta san cewa ni direba ne kuma motata ta lalace kafin mu yi aure. Hakan ne yasa na gaza kula da 'ya'yanmu. A lokacin da na samu mahaifiyarta don sanar mata da yadda take kyautar rashin hankali, mahaifiyarta ta ce kada in sake kawo karar diyarta saboda bata sanni ba."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel