'Yan APC 5,000 sun koma PDP a Edo, sun mara wa Obaseki baya

'Yan APC 5,000 sun koma PDP a Edo, sun mara wa Obaseki baya

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Edo ta samu koma baya a ƴunkurin ta na karbe mulki daga hannun jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Wannan na zuwa ne bayan mambobin APC fiye da 5,000 sun fice daga jam'iyyar sun koma PDP. Sun kuma jaddada goyon bayansu ga tazarcen Gwamna Godwin Obaseki.

Jagorar tsaffin ƴan Jam'iyyar ta APC da suka koma PDP a gunduma ta 6, Ubiaja, a ƙaramar hukumar Esan ta Gabas, Hon. John Bobby Palmer ya ce sun dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa Gwamna Obaseki ya ɗora kan ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

Da ya ke jawabi yayin taron yaƙin neman sake zaben gwamnan a Ubiaja, Shugaban na APC ya yaba wa Obaseki saboda fifita cigabar jihar a kan buƙatun wasu tsirarun ƴan siyasa marasa kishin jihar.

Yan APC 5,000 sun koma PDP a Edo, sun mara wa Obaseki baya
Yan APC 5,000 sun koma PDP a Edo, sun mara wa Obaseki baya. Hoto daga This Day
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

Palmer ya ce, "Obaseki ya taka rawar gani a wa'adin mulkinsa na farko kuma saboda muna son abin alheri, ba mu da zabi da ta wuce shiga jam'iyyar da ke kawo cigaba."

Shugaban, kamfen din PDP na Edo, Chif Dan Orbih ya ce: "Nasarorin da Obaseki ya yi cikin shekaru uku sun ɗara abinda Oshiomhole ya yi a shekaru takwas. Idan Obaseki ya koma mulki, za a dama da mutanen Esan a siyasar jihar Edo.

"A karkashin tsarin kawo canji a fanin ilimi (EDOBEST), ana koyar da dalibai fiye da 40,000 daga gidajensu a wannan lokacin annobar coronavirus din."

A bangarensa, Gwamna Obaseki ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da kawo canjin da shirye-shiyen da za su inganta rayuwar al'ummar jihar, inda ya ƙara da cewa, "bamu nuna banbanci domin dukkan ƴan Edo ɗaya su ke."

"Fifita wasu a kan wasu ba tsari bane mai kyau na siyasa, a wuri na, dukkan ƴan jihar nan ɗaya su ke a idon gwamnati na."

Gwamna ya ce ya bayar da kwangilar aikin titin Ubiaja-Ugboha kuma za a fara aikin bayan damina ta wuce.

Ya kuma kara da cewa cikin shekaru biyu gwamnatinsa ta yi nasarar kafa cibiyoyin samar da lantarki da suke samar da megawat 1,000 amma kamfanin lantarki na Benin, BEDC na cigaba da musguwanawa ƙoƙarin na gwamnatinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel