FG ta kashe 97% na kudin shigar wata 5 wurin biyan bashi

FG ta kashe 97% na kudin shigar wata 5 wurin biyan bashi

Gwamnatin tarayya ta kashe kashi 97.5 daga cikin kudin shiga na watan Janairu zuwa Mayun 2020 wurin biyan bashi, jaridar The Cable ta wallafa.

Kamar yadda kasafin kudin shekarar 2021 wanda ofishin kasafi ya wallafa, gwamnatin tarayyar ta samu kudin shiga har N1.62 tiriliyan daga cikin N2.62 tiriliyan da aka yi hasashen na wannan lokacin.

A cikin watanni biyar, N1.58 tiriliyan aka kashe wurin biyan bashi, kashi 97.5 na N1.62 tiriliyan kenan na kudin shigar.

A watan Yuni, bankin duniya ya bayyana cewa biyan bashi zai lamushe kudin shiga na gwamnatin tarayya na 2020.

Kamar yadda takardar ta nuna, gwamnatin tarayya ta kashe N3.98 tiriliyan a cikin watanni biyar, N1.79 tiriliyan an fitar da shi ne wurin ayyukan yau da kullum da suka hada da biyan albashi, kudin fansho da sauransu.

An fitar da N378.85 biliyan domin aiwatar da manyan ayyuka a cikin wannan lokacin.

Bayani game da kudin shigar da aka samu ya nuna cewa, N701.6 biliyan ya fito ne daga bangaren man fetur yayin da bangarorin da ba na man fetur ba sun samo N439.32 biliyan.

An samo N213.24 biliyan daga kudin harajin kamfanoni, N68.09 biliyan daga VAT, sai kuma N158 biliyan daga bangaren kwastam.

Dole ta sa aka sake duba kasafin kudin 2020 bayan faduwar farashin danyen man fetur, bayan rikici a kan farashi na kasar Rasha da Saudi Arabia da kuma annobar duniya ta korona.

Tsakanin watan Janairu zuwa Mayu, gwamnatin tarayya ta ci bashin N2.35 tiriliyan.

FG ta kashe 97% na kudin shigar wata 5 wurin biyan bashi
FG ta kashe 97% na kudin shigar wata 5 wurin biyan bashi. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da rana tsaka 'yan Indiya ke lalata da ma'aikata mata - Ma'aikatan kamfanin Atiku

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya za ta kashe naira tiriliyan 12.658 a matsayin kasafin kudin shekarar 2021.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sabuwar takardar manhajar tattalin arziki da ma’aikatar kudi, kasafi, da tsare-tsare ta fitar.

Takardar, mai dauke da sa hannun ministar kudi, Zainab Ahmed, ta nuna cewa adadin ya samu karin kaso 17.2 na kasafin kudin 2020; naira tiriliyan 10.8, da aka sake nazari daga baya.

Gaba daya jimillar kudaden shiga da ke kasa na kasafin kudin shekara mai zuwa an kimanta shi a kan naira tiriliyan N7.498 yayinda jimillar kudin da za a kashe an kiyasta shi a kan naira tiriliyan N12.658.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel