Buhari yana jagorancin taron FEC ta yanzar gizo karo na 13 (Hotuna)

Buhari yana jagorancin taron FEC ta yanzar gizo karo na 13 (Hotuna)

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yana jogarantar taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya, FEC karo na 13 da ake yi ta yanar gizo wato intanet karo na 13 daga gidan gwamnati da ke Abuja.

Taron da aka fara misalin karfe 10 na safe bayan shugaban kasar ya shiga dakin gudanar da taron na FEC ya samu hallarcin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Ministoci guda shida ne suka samu hallartar taron a zahiri cikinsu har da Ministan shari'a kuma Attoney Janar, Abubakar Malami; Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed; Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsare Tsaren Kasa, Zainab Ahmed.

DUBA WANNAN: Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

Sauran sun hada da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatude Fashola; Ministan Maadinai da Karafa, Olamiklekan Adegbite da Ministan Birnin Tarayya, Abuja, Mohammed Bello.

Sauran ministocin shugaban kasar sun hallarci taron daga ofisoshinsu ta hanyar yanar gizo.

Kazalika, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mr Boss Mustapha; Shugaban Maaikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari da Mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Babagana Monguno sun hallarci taron a zahiri.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164