Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu

Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu

Mahauta masu sana'ar nama a tsohuwar kasuwar Kurmi ta birnin Kano, sun ci gaba da jajanta rushe musu shaguna da aka yi a cikin karamar hukumar birni a jihar Kano.

Mahautan da ke kasuwar suna da shaguna 88, kuma an tabbatar da cewa kasuwar ta kwashe a kalla shekaru 120 kafin rusheta a makon da ta gabata.

A yayin zantawa a kan lamarin da ya faru, mataimakin shugaban kungiyar mahautan kasuwar, Alhaji Nasidi Nafi'u Yahaya, ya ce a cikin sa'o'i shida kacal aka rushe kasuwar.

"Da farko sun ce sun bamu kwanaki uku mu kwashe kayanmu daga shagunan, amma bayan sa'o'i uku kacal, sun zo sun fara rushe mana shagunan ba tare da wata takardar shaida ba," Yahaya ya ce.

“A matsayina na mataimakin shugaban kungiyar mahauta na shekaru 28, ina tabbatar muku da cewa ban san wani abu a kan rusau din nan ba.

"Sun kawo 'yan daba dauke da miyagun makamai kuma sun tirsasa mu barin shagunanmu kafin daga bisani sun rushesu," ya kara da cewa.

Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu
Rusau a Kano: Mahauta sun koka da yadda aka nike shagunansu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa

Mataimakin shugaban kungiyar mahautan ya kara da zargin cewa sabbin shagunan da za a gina tuni aka raba wa wasu mutane, wadanda ya ce ba a cikin kasuwar suke ba.

Ya ce tun bayan rushe shagunan, mahautan sun koma rabewa shagunan jama'a saboda basu da inda za su je.

Hakazalika, Sharu Jibrin, wanda ya ce ya kwashe shekaru 65 a kasuwan, ya kara da cewa shugabannin mahautan a jihar sun karba fasfotinsu tare da alkawarin hada musu shagunan wucin-gadi.

"Suna rushe shagunan ne tare da lalata kadarorinmu. A saboda haka, faduwa nayi, jikokina suka kai ni gida. A yanzu an mayar da mu marasa aikin yi," yace.

Wani mahauci a kasuwar mai suna Sanusi Musa, ya ce ya kwashe sama da shekaru 45 a kasuwar bayan da ya gaji shagon daga mahaifinsa wanda ya gada daga kakanninsa.

"Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya sake duba wannan lamarin saboda bamu da wurin zuwa," Musa yace.

Sakataren kungiyar mahautan, Abba Abdullahi Sani Korau, ya ce za su nema hakkinsu a kotu.

Amma kuma gwamnan ya musanta hannunsa a cikin rushe shagunan, inda yace bai san da wannan ci gaban ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel