Yadda N300 ya yi sanadiyar rasuwar mutum 12 a cikin jirgin ruwa a Legas

Yadda N300 ya yi sanadiyar rasuwar mutum 12 a cikin jirgin ruwa a Legas

- Wani direban jirgin kasa ya yi sanadiyar mutuwar fasinjojinsa 12 a jihar Legas

- Hakan ya faru ne bayan direban ya kashe jirgin a tsakiyar rafi ya yi karin kudin jirgi

- Wannan karin da direban ya yi daga N1,200 zuwa N1,500 kwatsam a tsakiyar ruwa ya harzuka fasinjojin

Kwamishinan Yan Sanda a Jihar Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata ya bayar da bayanin yadda wani mai haya da jirgin ruwa, Elebiju Bimbo ya yi sanadin mutuwar mutum 12 cikin fasinjojin da ya dakko.

Daily Trust ta ruwaito cewa Bimbo ya dage ne cewa sai ya karbi N1,500 a maimakon N1,200 a matsayin kudin jirgi daga hannun fasinjojin wadda hakan ya janyo cece kuce.

Yadda N300 ya yi sanadiyar rasuwar mutum 12 a Legas
Yadda N300 ya yi sanadiyar rasuwar mutum 12 a Legas. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

Odumosu ya yi bayanin cewa mai jirgin ya dako fasinjojinsa ne daga wani gabar ruwa a Kirikiri kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Badagry kwatsam a tsakiyar rafi sai ya kashe jirgin ruwan ya kara kudi daga N1,200 zuwa N1,500.

Shugaban yan sandan ta jihar Legas da ya gabatar da wanda ake zargin ga manema labarai ya ce wannan karin kudin da direban jirgin ya yi ya janyo cece kuce tsakanin fasinjojin da direban.

Ya ce jirgin ya yi ta matsa wa har sai da ya yi karo da wani jirgin daukan kaya bayan wani babban jirgi da ke bankado ruwa ta gefen su.

A lokacin da hatsarin ya faru, mutane 20 ke cikin jirgin kuma daga cikinsu mutum takwas ne kawai suka tsira da rayyukansu hakan ke nuna mutum 12 sun riga mu gidan gaskiya.

A wani rahoton daban, Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa na kasar Portugal ya bada mamaki yayin da ya fada cikin rafi ya ceto wasu mata biyu da ke nutsewa a ruwa a Algarve beach bayan da jirginsu ya kife.

A cewar BBC, an dauki hotunan shugaban kasar mai shekaru 71 yayin da ya fada cikin rafin ya ceto matan da ke kokarin kada su nutse.

De Souse daga bisani ya shaidawa manema labarai cewa ruwa ne ya kwaso matan daga wani rafi da ke kusa da inda ya ke.

Shugaban kasar na Portugal a halin yanzu yana hutu ne wurin shakatawa ta Algarve da nufin janyo hankalin masu yawon bude ido zuwa wurin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel