Katsina: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidaje 1,727 a Baure

Katsina: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidaje 1,727 a Baure

- Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina, ta sanar da cewa gidaje 1,727 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Baure

- Babangida Nasamu, shugaban hukumar, ya tabbatar wa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jihar Katsina

- Ya tabbatar da mazauna yankin cewa hukumar za ta bada tallafin wurin zama da kayan rage radadi ga wadanda abun ya shafa

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Katsina (SEMA) ta ce gidaje 1,727 ne ta yi wa rijista wadanda ambaliyar ruwa ta kwashewa gidaje a karamar hukumar Baure ta jihar.

Shugaban hukumar, Babangida Nasamu, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Baure, cewa gidaje 1,626 ne da suka rushe sakamakon mamakon ruwan saman da aka yi.

Ya ce ambaliyar ruwan ta shafi kauyukan Unguwar Rai, Hui, Yanduna, Kawarin Gyada da Dawaye yayin da gonaki 101 suka lalace a karamar hukumar.

Ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa hukumar za ta samar wa wadanda abun ya shafa matsuguni da kayan tallafi kafin su fara gyaran gidajen.

Katsina: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidaje 1,727 a Baure
Katsina: Ambaliyar ruwa ta kwashe gidaje 1,727 a Baure. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Kamar yadda yace, hukumar za ta fara raba kayan rage radadi ga wadanda abun ya shafa.

Daya daga cikin wadanda abun ya shafa, Malam Mamman Mujittaba, ya jinjinawa kokarin gwamnatin wurin samar da muhallin wucin-gadi ga jama'ar yankin.

Fiye da iyalai 300 ne a kauyuka 6 suka rasa gidajensu a karamar hukumar Amawbia dake jihar Anambra sakamakon ambaliyar ruwa.

Ambaliyar tare da zai-zayar kasa ta shafi kauyuka da dama inda ta datse hanyoyin da ke tsakaninsu da biranen da suke da makwaftaka dasu irin su Nise, Nibo, Umuokpu da Agukwu Nnri.

Zai-zayar kasar ta hana yara zuwa makarantunsu. Hakazalika, yara biyu ne suka tsallake rijiya da baya sanadiyar ambaliyar domin kiris da ruwan yayi gaba da su.

Maduforo ya kara da cewa "Matanen Awambia da mazauna wajen sun kashe sama da naira miliyan 800 a shekaru 7 da suka gabata don yakar matsalolin muhalli ba tare da tallafin gwamnati ba."

Sauran yankunan da zai-zayar kasar ta shafa ya hada da: Makarantar sakandare ta Union, Kwalejin Kabe, Otal din May Rose, inda duk hanyoyin da zasu kai garesu sun lalace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel