Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira

Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira

- Sheik Ibrahim Zakzaky ya raba tallafin magunguna da gidajen sauro ga mazauna sansanonin gudun hijira a Faskari, jihar Katsina

- Sheik Rabiu Abdullahi Funtua ya ce Sheik Zakzaky zai ci gaba da bada tallafi duk da yana a kulle

- Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun godewa Sheik Zakzaky da irin kokarinsa, tare da addu'ar Allah ya sa a sake shi

Shugaban mabiya akidar Shi'a, Sheik Ibrahim Zakzaky a ranar Talata ya raba tallafin magunguna da gidajen sauro ga mazauna sansanonin gudun hijira a karamar hukumar Faskari, jihar Katsina.

Wakilin Sheikh Zakzaky a Funtua, Sheik Rabiu Abdullahi ya ce shehin ya zabi sansanin Faskari domin tallafawa mazauna sansanin da suka bar garuruwansu sakamakon hare haren 'yan bindiga.

"Mun ji dadin ganin yadda iyaye mata da kuma wasu rukunin matan da suka zo karbar gidajen sauron da magunguna a cikin sansanin 'yan gudun hijirar," a cewarsa.

Ya ce wannan tallafin anyi shi ne domin nuna soyayya da jin kai, tare da nuni da cewa Sheik Zakzaky zai ci gaba da bada tallafi duk da yana a kulle, musamman a wannan yanayi.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saki jagoran nasu domin duba lafiyarsa, yana mai cewa "tun bayan kisan gillar da gwamnati ta yiwa 'yan uwanmu a Zaria muka yi kira ga jama'armu cewa idan an taba mutum daya, kamar dukanmu ne aka taba."

KARANTA WANNAN: Shugaban kasar Mali, Ibrahim Keita, ya yi murabus

Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira
Sheik Zakzaky ya raba magunguna da gidajen sauro a sansanonin 'yan gudun hijira
Asali: UGC

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun godewa Sheik Zakzaky da irin kokarinsa, tare da addu'ar Allah ya sa a sake shi.

A wani labari, Shugaban kasar Mali a ranar Laraba ya ce ya yi murabus domin hana "zubar da jini", awanni bayan da rundunar soji suka yi caraf da shi, a yunkurin juyin mulki.

Cafke shugaban kasar da yunkurin juyin mulkin, yana zuwa ne bayan shafe sama da watanni ana rikicin siyasa a kasar Mali.

Sojojin hamayya sun cafke Ibrahim Boubacar Keita da Firam Minista Boubou Cisse a ranar Talata, tare da tsaresu a wani sansanin soji da ke garin Kati, kusa da Bamako, babban birnin kasar.

Dandanzon mutane ne suka taru don nun murnarsu na tsare Keita, tare da bukatar dole sai yayi murabus, a lokacin da sojojin suka kutsa kai gidan tsohon shugaban kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel