Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari

Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari

- Wata kotun Shari'ar Musulinci dake Kano ta yankewa yaro dan shekara 13 hukuncin shekaru 10 a gidan gyara hali

- Kotun ta kama yaron da laifin kalaman batanci ga Allah

- Alkalin da ya yankewa Sharif Aminu hukuncin kisa ne ya yankewa wannan yaro hukunci

Wata babbar kotun Shari'ar Musulinco dake zamanta a jihar Kano ta yankewa wani yaro dan shekara 13 da haihuwa, Umar Farouq, hukuncin shekaru 10 a kurkuku kan laifin batanci ga Allah.

Alkali Aliyu Kano ya kama Umar Farouq da laifi ne ranar 10 ga Agusta, 2020.

Shine Alkalin da ya yankewa Sharif Aminu, mawakin da yayi kalaman batanci ga manzon Allah hukuncin kisa.

A cewar Daily Mail, kotu ta yanke wannan hukunci ne kan laifin kalaman da bai dace ba ga Allah.

Kakakin ma'aikatar Shari'ar jihar, Baba-Jibo Ibrahim, ya ce an yankewa yaron hukuncin shekaru 10 ne saboda kalaman da ya furta yayin musu da wani abokinsa.

Ibrahim ya ce kotun ta yi la'akari da shekarun Farouq, shi yasa ta yanke masa hukunci dauri a kurkuku domin ya gyaru.

Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari
Batanci ga Allah a Kano: Kotu ta yankewa yaro dan shekara 13 daurin shekaru 10 a gidan yari
Asali: Twitter

A bangare guda, Kungiyar Lauyoyi Musulmai a jihar Kano (MULAN), ta yabwa kotun Shari'ar Musulunci kan yankewa Yahaya Sharif Aminu hukuncin kisa kan kalaman batanci ga manzon Allah (SAW)

Kungiyar Lauyoyin a takardar da shugabanta, Muhammadu Sani Garba, ya saki, ya ce Alkalin ya yi daidai a hukuncin da ya yanke na kisa ba tare da hanashi iya daukaka kara ba saboda kotun koli ta yanke irin hukuncin a shari'ar Abubakar Shalla Vs State a 2007.

Kungiyar MULAN ta yi kira ga gwamna Ganduje ya rattafa hannu kan hukuncin, amma har yanzu gwamnan bai yi tsokaci ba.

Shugaban MULAN yace: "Abinda dokar Shari'ar Musulunci ta tanada shine duk wani Musulmi baligi, wanda ya zagi manzon Allah, ko kalaman batanci ga manzon Allah, ya aikata laifi mai girma kuma ya cancanci kisa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel