Zaben Ondo: Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya zabi abokin takararsa

Zaben Ondo: Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya zabi abokin takararsa

- Mr Eyitayo Jegede ya zabi Hon. Ikengboju Gboluga a matsayin abokin takararsa

- Mr Jegede shine dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar PDP

- Za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo ne a ranar 10 ga watan Oktoba, 2020

Dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede ya zabi Hon. Ikengboju Gboluga a matsayin abokin takararsa.

Mr. Jegede ya sanar a hakan a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Hon. Ikengboju Gboluga zai yi takara tare dani a babban zaben jihar da za a gudanar ranar 10 ga watan Oktoba 2020," a cewarsa.

Hon. Gboluga ya kasance mamba ne a majalisar wakilan tarayya da ke wakiltar mazabar Okitipupa/Irele a majalisar tarayya.

Wannan na zuwa awanni 24 bayan da dan takarar jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP) a jihar Ondo, Agboola Ajayi, ya zabi nasa abokin takarar don fuskantar zaben jihar.

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta magantu kan ranar bude jami'o'i

Zaben Ondo: Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya zabi abokin takararsa
Zaben Ondo: Dan takarar gwamna karkashin jam'iyyar PDP ya zabi abokin takararsa
Asali: Twitter

Ajayi wanda ya kasance mataimakin gwamnan jihar ya zabi Gboye Adegbenro a matsayin abokin takararsa.

Mataimakin gwamnan, a makon da ya gabata ne ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar ZLP a Akure, babban birnin jihar.

A wani labarin; Gwamnatin tarayya ta ba kungiyar dalibai ta kasa (NANS) tabbacin cewa za a bude makarantu da suka hada da jami'o'i da zan an samu damar yin hakan.

Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bada tabbacin a wani taron bita na kwamitin a ranar Litinin.

Ya ce a ranar Litinin dalibai suka fara zana jabawarar kammala makarantar sakandire, kuma kwamitin PTF na farin ciki na yadda makarantun suke kiyaye dokoki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel