Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa

Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sha caccaka daga wajen jama'a a kafafen sada zumuntar zamani a kan ikirarin da yayi na cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashawa ba.

A ranar Asabar, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, Ganduje ya sanar da hukumar sauraron korafi da yaki da rashawa ta jihar cewa ba zai bar duk wani mai cin rashawa a jihar ba ya tafi a sake.

Gwamnan ya yi alkawarin cewa ba zai saka baki a kan kowanne zargin rashawa da ake wa kowa ba a jihar.

Amma kuma, a 2018, jaridar Daily Nigerian ta samu wasu bidiyo na Ganduje inda yake kalmashe daloli a matsayin rashawa daga hannun wani dan kwangila a jihar.

Bidiyon, wanda ya fito daga dan jaridar nan fitacce na jihar Kano, Jafaar Jafaar, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, sun yi tsit a kai.

A yayin da shugaban kasa ya yi magana a kan bidiyon, ya saka wasu-wasi a kan ingancin bidiyon ba tare da bada umarnin bincikarsa ba.

Majalisar jihar ce kadai ta yi yunkurin daukar mataki a kai. A maimakon Ganduje ya bar majalisar ta bincika, ya dakatar da majalisar inda ya samo umarnin kotu wanda ya dakatar da su.

A yayin wannan zargin, an sake zaben gwamnan a karo na biyu, kuma a halin yanzu haka yana more kariyar da kujerarsa ta bashi.

Fusatar da jama'a suka yi da tsokacin Ganduje a kan rashawa na ranar Asabar, 'yan Najeriya sun zargesa da niyyar nuna walittakarsa.

Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa
Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa. Hoto daga The Cable
Source: UGC

KU KARANTA: Ka fada wa jama'a malaman da ke son kudi ko ka rufe mana baki - Fasto ya caccaki El-Rufai

Ga wasu daga cikin tsokacin da jama'a suke yi:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel