Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Hotuna)

Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa na kasar Portugal ya bada mamaki yayin da ya fada cikin rafi ya ceto wasu mata biyu da ke nutsewa a ruwa a Algarve beach bayan da jirginsu ya kife.

A cewar BBC, an dauki hotunan shugaban kasar mai shekaru 71 yayin da ya fada cikin rafin ya ceto matan da kekokarin kada su nutse.

De Souse daga bisani ya shaidawa manema labarai cewa ruwa ne kwaso matan daga wani rafi da ke kusa da inda ya ke.

Shugaban kasar na Portugal a halin yanzu yana hutu ne wurin shakatawa ta Algarve da nufin janyo hankalin masu yawon bude ido zuwa wurin.

Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Photos)
Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Photos)
Asali: Twitter

Yawon bude idanu na daya daga cikin manyan hanyoyin da kasar ta Portugal ta dogara da shi domin samun kudaden shiga sai dai an samu tsaiko sosai saboda annobar korona ta hana tafiye tafiye.

Shugaban kasar ya hangi matan suna nutsewa a ruwa jim kadan bayan ya gama magana da manema labarai a Praia do Alvor beach.

Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Photos)
Shugaban kasar Portugal ya fada cikin ruwa ya ceto mata biyu (Photos)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An buƙaci Buhari ya nemi taimako daga wurin mayu don samar da tsaro da kawar da rashawa

An nadi bidiyon lokacin da shugaban kasar ya yi nunkaya cikin ruwan domin zuwa ya taimaka musu.

Bayan ya ceto su, Shugaban Sousa ya shaidawa manema labarai cewa, "Ruwa mai karfi ne daga teku ya turo su, an ciro su daga ruwan, an juya su, sun sha ruwa sosai har ta kai ga sun gaza hawa jirginsu ko yin iyo, haka karfin ruwan ya ke."

Shugaban kasar ya ce wani dan kasa na gari ya taimaka masa wurin ceton su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel