Basaraken da 'yan bindiga suka sace a Yobe ya samu 'yanci

Basaraken da 'yan bindiga suka sace a Yobe ya samu 'yanci

Wadanda suka yi garkuwa da dagajin kauyen Mashio a karamar hukumar Fune ta jihar Yobe, Isa Mashio sun sako shi kamar yadda yan sanda suka bayyana a ranar Talata.

An sace dagajin ne a daren ranar Asabar yayin da yan bindiga suka kawo hari garin suka rika harbe harbe a daren ranar Asabar.

Wata sanarwar da mai magana da yawun yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkareem ya fitar ta ce wadanda suka sace shi sun yarda shi a wani fili da ke kusa da babban birnin jihar wato Damaturu.

Basaraken da 'yan bindiga suka sace a Yobe ya samu 'yanci
Basaraken da 'yan bindiga suka sace a Yobe ya samu 'yanci
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara

Sakon ya ce, "Barka da safe, muna farin cikin sanar da ku cewa an ceto Alhaji Isa Mai Buba a yau 18/8/2020 kimanin karfe 6 na safe daga wurin wadanda suka sace shi.

"Hakan ya faru ne sakamakon kwazon da hadakar hukumomin tsaro na jihar suka yi inda suka rufe dukkan hanyoyin fita daga jihar aka kuma tsaurara matakan tsaro hakan yasa wadanda suka sace shi suka sako shi domin ba su da inda za su iya zuwa. Daga bisani sun sako shi a wani fili kusa da filin jiragen Gashua a Damaturu."

A wani labarin mai kama da wannan da Legit.ng Hausa ta wallafa, an ceto iyalan mariagyi Musa Mante Baraza, dan majalisar Bauchi da aka kashe kuma aka yi garkuwa da matarsa da dan sa mai shekara daya.

Labarin sakinsu an same shi ne daga bakin shugaban ma'aikatan fadar gwamnan jihar Bauchi, Dr Kadan Salihu.

Ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce, "Alhamdulillah! An sako matan dan majalisar jihar Bauchi da aka kashe a kwanaki hudu da suka gabata."

Ladan ya kara da cewa, "dan shi mai shekara dayan da aka sace tare da su duk an sako su.

Gwamna Bala Mohammed ya bai wa likitoci da jami'an tsaro umarnin basu kulawa da tsaro.

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin saboda su suka ceto wadanda aka sacen.

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin saboda su suka ceto wadanda aka sacen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel