Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai cutar korona ke rubuta jarabbawar SSCE a Gombe

Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai cutar korona ke rubuta jarabbawar SSCE a Gombe

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bada izinin daliban sakandare da ke babban ajin karshe wato ss3 da karamin ajin karshe jss3 su dawo makaranta su rubuta jarrabawar fita wato SSCE.

Biyo bayan matakin da gwamnatin tarayyar da dauka, jihohin Najeriya su ma sun bi sahun bude makarantun domin daliban su rubuta jarrabawar fitan.

Sai dai kafin a bude makarantun, gwamnatin tarayya da maaikatan lafiya da kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar korona duk sun bayar da kaidoji da makarantun za su bi don kiyaye lafiyar dalibai da malamansu.

Sai dai a jihar Gombe akwai wani dalibi da ke ajin karshe wato ss3 kuma yana dauke da cutar ta korona.

Gwamnatin jihar ta Gombe da bashi damar ya rubuta jarrabawar daga cibiyar killace masu dauke da cutar ta korona a jihar.

An kuma tanadi malami mai kula da shi yayin da ya ke rubuta jarrabawar inda shima aka bashi kayan kare kansa daga kamuwa daga cutar ya saka sannan ya shiga domin bawa dalibin takardan jarrabawar kuma ya tsaya ya jira dalibin ya gama.

Ga dai hotunan dalibin da mai kula da shi a kasa.

Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai korona ke rubuta SSCE a Gombe
Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai korona ke rubuta SSCE a Gombe. Hoto daga @GombePHEOC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai korona ke rubuta SSCE a Gombe
Hotuna: Yadda dalibin sakandare mai korona ke rubuta SSCE a Gombe. Hoto daga @GombePHEOC
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, rahotanni sun ce an tabbatar da cewa Hakimin garin Kufana a kasar Kajuru, jihar Kaduna, Mista Titus Dauda ya kamu da cutar COVID-19.

Daily Trust ce ta fitar da rahoto cewa Titus Dauda ya na dauke da kwayar cutar COVID-19. An tabbatar da wannan ne a ranar 17 ga watan Agusta, 2020.

Jaridar ta ce tun kafin yanzu, Titus Dauda ya na ta fama da zazzabi. A dalilin haka ne aka garzaya da shi zuwa wani asibiti a makon da ya wuce.

A asibitin ne aka tabbatar da cewa Hakimin na Kufana ya kamu da cutar COVID-19. Wannan Basarake ya shiga sahun wadanda annobar ta kwantar a Kaduna.

A wani jawabi da ya fito daga fadar hakimin a ranar Asabar, ya bayyanawa Duniya cewa ya na dauke da kwayar COVID-19 mai jawo wahalar numfashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel