Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta

Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta

- Wata mata ta wallafa hotunan ta biyu da suka tada hankalin ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani

- A hotunan, wata kyakyawar mata ta bayyana sanye da kayan alfarma tare da kek inda take murnar mutuwar aurenta

- 'Yan kasar Afrika ta Kudun sun matukar girgiza da abinda ya faru inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu

Wata mata ta ja hankalin jama'a a kafar sada zumuntar zamani bayan da ta yi bikin shagalin murnar mutuwar aurenta.

A ranar Litinin, 17 ga watan Augusta, wata ma'abociyar amfani da Twitter mai suna Lungi Shozi, ta wallafa hotunan.

Matar ta siya wa kanta kek inda aka rubuta: "Na yi, na gama, na kammala. Mun rabu daga karshe."

Shozi ta yi rubutu kamar haka a kasan hotunan: "A yanzu jama'a har bikin shagalin mutuwar aure ake yi."

'Yan kasar Afrika ta Kudu sun kasa kyale hotunan a haka, amma sai suka bi sashen tsokaci inda suka dinga tofa albarkacin bakinsu.

Malusi luso ya yi tsokaci kamar haka: "Duniya yanzu ta aminta da rashin hankali. Duba, ba shagalin a kan kwanciyar hankali take yi ba, bacci ba tare da kuka ba, rashin dukan miji da sauransu."

Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta
Tirkashi: Hotunan matar da ta yi shagalin mutuwar aurenta. Hoto daga @IamlungiDee
Asali: UGC

KU KARANTA: Boko Haram: Sojoji sun ragargaza maboya da kayan aikin 'yan ta'adda a Borno

Duk da ba wannan bane karo na farko da aka fara shagalin murnar mutuwar aure ba, wani mutum ya bayyana na shi.

A kwanakin baya, bawan Allan ya fito inda ya nuna farin cikinsa bayan rasuwar aurensa.

Matashin ya sanar da rabuwarsa da matarsa inda ya ce ya dawo daga kangi. A wasu hotunan mutumin da suka bayyana, an gan shi tsaye a gaban wata babbar mota inda aka rubuta "yanzu mun rabu" ta tagar bayan motar.

A bayyane murnar mutuwar aurenshi ya ke a fuskar matashin kuma hotunan sun ba zu a kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel