Da duminsa: Wasu yan bindiga sun budewa gwamnan Imo wuta

Da duminsa: Wasu yan bindiga sun budewa gwamnan Imo wuta

Hukumar yan sanda a jihar Imo sun damke mutane 15 da ake zargin sun kaiwa gwamnan jihar, Hope Uzodinma, hari ranar Litnin, 18 ga watan Agusta, 2020.

Harin ya auku ne yayinda gwamnan yake hanyar tafiya kaddamar da sabon barikin Sojin da gwamnatin jihar ta gina a 34 Attilary Brigade, Obinze, The Nation ta ruwaito.

Yan bindigan, rike da bindigogi da adduna, sun yi ikirarin cewa su ma'aikatan hukumar cigaban garuruwa masu arzikin man fetur a jihar Imo (ISOPADEC) ne kuma suna zanga-zanga bisa rashin biyansu albashi.

Kwamishanan yan sandan jihar, Isaac Akinmoyede, ya ce yan bindigan sun yi ikirarin cewa su ma'aikatan ISOPADEC kuma an hanasu albashi watanni uku.

Ya ce an damkesu da karamar bindiga daya, adduna biyu, amawali daya, tsarka da kwado.

Akinmoyede yace: "Sun kaiwa jerin motocin gwamnan hari da karamar bindiga da kuma adduna."

Ya ce harin da ya auku bai yi sanadiyar mutuwar kowa ba.

"Amma an fasa gilasan motocin gwamnan kuma an lalata motoci," Yace

Ya ce tuni an mika yan bindigan sashen binciken hukumar domin cigaba da binciken lamarin.

KU KARANTA: Bayan sa'o'i 5, Hukumar DSS ta saki Ghali Na'abba

Da duminsa: Wasu yan bindiga sun budewa gwamnan Imo wuta
Da duminsa: Wasu yan bindiga sun budewa gwamnan Imo wuta
Asali: UGC

Gwamnatin jihar tace matsayarta kan ire-iren wadannan zanga-zangan cewa aikin abokan adawa ne ya tabbata.

Kwamishanan labaran jihar, Declan Emelumba, ya ce yawancin zanga-zangan da ake yi a jihar Siyasa ne.

Kwamishanan yace yan adawa sun dau hayan yan ta'adda ne sakamakon irin yabon da gwamnan ke samu bayan kaddamar da sabbin tituna a Owerri ranar Juma'a.

Ya yi kira ga yan sanda sun bayyana wadanda ke daukan nauyin wadannan yan bindigan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel