Na’Abba: Abin da yasa DSS ta gayyace ni

Na’Abba: Abin da yasa DSS ta gayyace ni

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Ghali Na'Abba ya ce hukumar ƴan sandan farin kaya, DSS, ta gayyace shi ne don ya yi ƙarin bayani a kan wasu maganganu da ya furta.

Tsohon Kakakin Majalisar ya ziyarci hedkwatar hukumar DSS da ke Abuja a ranar Litinin.

Ƴan sandan farin kayan sun gayyaci Na'Abba ne kwanaki hudu bayan ya furta wasu kalamai na caccakar gwamantin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wata shirin talabijn na kai tsaye da ya yi, Na'Abba wanda daya daga cikin wadanda suka kada sabuwar kungiyar kawo canji a kasa (NCFront) ya ce a halin yanzu Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka gaza.

Na’Abba: Abin da yasa DSS ta gayyace ni
Na’Abba: Abin da yasa DSS ta gayyace ni
Asali: UGC

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan ziyarar, Na'Abba ya ce hukumar tsaron ta gayyace shi ne don ya yi ƙarin haske game da abinda ya ke nufi da wasu kalmomi da ya furta yayin hirar da aka yi da shi.

Tsohon ɗan majalisar ya ce hukumar ta masa tarba mai kyau kuma ya ji daɗin ziyarar da ya kai.

DUBA WANNAN: Terkimbi Ikyange: Tsohon Kakakin Majalisar Benue zai dawo APC

"Ban janye maganganun da na yi ba. Ba zan taɓa janye kalamai na ba. Na kan fadi gaskiya duk inda na gan ta. Wannan shine abinda na faɗa yayin hirar da aka yi da lokacin jawabin da na yi wa manema labarai. Ba zan yi karya ba," in ji shi.

"Abinda ya faru shine akwai wasu kalmomi da na yi amfani da su yayin jawabin da nayi da ke buƙatar karin haske kuma na tafi na fayyace musu abinda na ke nufi.

"Dukkan mu mun gamsu da abinda ya faru. Mun shawarci juna. DSS suna da aikinsu da irin kwarewar su. Nima ina da aiki na da kwarewa ta. Duk mun ƙaru da juna.

"Haka ya kamata al'ammura su kasance. Na ji dadin ziyarar da na kai. Bani da wata matsala kan yadda suka tarbe ni.

"A jawabi na, na yi amfani da wasu kalamai kamar 'ƙasar da ta gaza' da 'neman ƴancin kai'. Da na fadi kalmomin, abinda na ke nufi da su ya bambanta da yadda wasu suka ɗauke su.

"Neman ƴanci a wannan muhallin na nufin duk ƴan Najeriya suna da ikon suyi rayuwar su ta yadda suke so.

"Baya nufin a raba ƙasa. A lokuta da dama idan wasu sun furta wannan kalmar suna nufin raba ƙasa amma ba haka na ke nufi ba. Wannan shine karin bayanin da na yi.

"Ƙasar da ta gaza ita ce duk wata ƙasa da ba za ta iya samar wa mazauna kasar wasu abubuwa ba. Abinda ya faru shine a ra'ayinsu ban yi amfani da kalmar a inda ta dace ba kuma shi ɗan adam yana iya amfani da kalma a wurin da ba ta dace ba kuma na faɗa musu abinda na ke nufi da abubuwan da suka sa na danganta Najeriya da kalmar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel