Wada Maida: Tsohon sakataren watsa labaran Buhari ya rasu

Wada Maida: Tsohon sakataren watsa labaran Buhari ya rasu

- Allah ya yi wa tsohon sakataren watsa labaran Shugaba Muhammadu Buhari rasuwa

- Marigayi Wada Maida ya rasu ne a garin Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya kamar yadda iyalansa suka sanar

- Malam Wada Maida ya rasu ne yana da shekaru 70 a duniya

Tsohon sakataren watsa kabaran Shugaba Muhammadu Buhari kuma shugaban Kwamitin Direktocin People’s Media, Malam Wada Maida ya rasu.

Iyalansa sun tabbatar da rasuwar tsohon babban edita kuma shugaban kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN a ranar Litinin.

Ya rasu ne misalin karfe 10:00 na dare a babban birnin tarayya Abuja bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Wada Maida: Tsohon sakataren watsa labaran Buhari ya rasu
Wada Maida: Tsohon sakataren watsa labaran Buhari ya rasu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An naɗa Buratai Ƙauran Gusau a jihar Zamfara

Wata majiya daga iyalan mamacin ta shaidawa Daily Trust cewa marigayin ya dawo daga Katsina a ranar Litinin bayan zuwa yi wa wani daga cikin abokansa taaziyar rasuwar matarsa.

Marigayin na da hannun jari a Media Trust Limited.

Kafin rasuwarsa, Maida ne shugaban direktocin NAN kuma mamba ne a kwamitin cibiyar yan jarida ta kasa da kasa.

Maina ya yi bikin cika shekaru 70 a watan Maris na shekarar 2020.

A wani labarin da Legit.ng Hausa a wallafa, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya zuwa ga iyali da rundunar soji bisa mutuwar Manjo Janar Samaila Iliya.

A cikin wani jawabi da ya fitar ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, Buhari ya bayyana janar Iliya a matsayin mutunin da ya sadaukar da rayuwarsa domin hidimtawa kasarsa kafin ya yi ritaya.

Kazalika, shugaba Buhari ya sake mika sakon ta'aziyya ga abokan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya kasance shugaba abin koyi a lokacin da ya rike mukamai ma su yawa a rudnunar soji.

Buhari ya yi waiwaye a kan irin nasarar da janar Iliya ya samu a lokacin da ya jagoranci tawagar sojojin Najeriya da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a Rwamda da Lebanon.

A cewar Buhari, jarumtar janar Iliya ta sa an nada shi jagorantar tawagar rundunar sojojin kasashen duniya da majalisar dinkin duniya ta tura jamhiriyar Domokradiyyar Kongo (DR Congo) domin tabbatar da zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel